Wata Sabuwa: Fastocin Tinubu, Gwamna Abba da Sarki Aminu Bayero Sun Mamaye Kano

Wata Sabuwa: Fastocin Tinubu, Gwamna Abba da Sarki Aminu Bayero Sun Mamaye Kano

  • Hotunan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Gwamna Abba Kabir Yusuf da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, sun mamaye wasu muhimman wurare a birnin Kano
  • An ga fastocin a kan titin State Road da ke kaiwa zuwa gidan gwamnatin Kano da fadar Nassarawa, inda Bayero yake zaune a halin yanzu
  • An kuma ga fastocin a kan titin Emirs Palace Road, wanda ke kaiwa zuwa fadar Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Fastocin da ke ɗauke da hotunan Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu; Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf; da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, sun mamaye wasu muhimman wurare a cikin birnin Kano.

Wannan fastoci sun mamaye tituna daban-daban a Kano yayin da ake shirye-shiryen babban zaben 2027, wanda za a fara a ranar 16 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Wani faifan bidiyo na neman jefa ɗan majalisar Kano a gagarumar matsala

Abba.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da wata fasta mai dauke da hotonsa, Tinubu da Sarki Aminu Ado Bayero Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

An lika fastocin Abba, Tinubu da Aminu

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an ga fastocin a kan titin State Road, wanda ya nufi gidan gwamnatin Jihar Kano da kuma fadar Nassarawa, inda Bayero yake zaune a halin yanzu.

Haka zalika an kuma ga fastocin a kan titin Emirs Palace Road, wanda ya nufi fadar da Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, yake zaune a Kofar Kudu da ke cikin birnin Kano.

Wuraren da aka manna fastocin suna da muhimmanci, kasancewar sun haɗa da hanyoyin da ke kewaye da gidan gwamnatin jihar da kuma fadojin sarakunan biyu.

Mene ne dalilin lika fastocin a Kano?

Wannan al'amari na zuwa ne a daidai lokacin da takaddamar sarautar gargajiya a Kano ke ci gaba da ɗaukar hankali, yayin da ake dakon hukuncin da kotun koli za ta yanke.

Sai dai ba a bayyana dalilin manna fastocin nan take ba, ko kuma ko wani gangamin yaɗa saƙo ne da aka tsara tare da haɗin gwiwa.

Kara karanta wannan

Rigima ta shiga gwamnatin jihar Kano tsakanin wasu hadiman Abba Gida Gida

Babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnati ko bangaren fadar Nassarawa da Sarki Aminu ke ciki, haka zalika babu wata kungiyar fararen hula da ta siyas da ta dauki nauyin lika fastocin.

Fastoci.
Yadda aka lika fastoci dauke da hotunan Shugaba Bola Tinubu, Gwamna Abba Kabir Yusuf da Aminu Ado Bayero Hoto: Dailytrust
Source: Facebook

Wannan lamari ya faru ne a yayin da ake ci gaba da takaddama kan sarautar Kano, wadda ta jima tana jan hankalin jama’a tun bayan mayar da Sanusi II kan karagar sarauta da kuma jerin ƙalubalen shari’a da siyasa da suka biyo baya.

Bayyanar fastocin Sarki Aminu Bayero, Tinubu da Gwamna Abba Kabir Yusuf a wurare guda ta ƙara wani sabon salo ga sauye-sauyen siyasa da al’amuran gargajiya da ke faruwa a jihar Kano.

Sanusi II ya roki Gwamna Abba alfarma

A wani labarin, kun ji cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya tura alfarma ta musamman ga Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Abba Kabir .

Sarkin ya bukace shi da ya biya diyya ga ’yan kasuwar da rusau ya shafa a kasuwar Filin Idi, da ke Kofar Mata, Kano , tare da sake ware musu wuraren kasuwanci.

Sanusi II ya rubuta wasiƙa ga Gwamna Abba Yusuf, yana neman a biya ’yan kasuwar diyya tare da ɗaukar matakan da za su rage asarar tattalin arzikin da suka yi sakamakon rusau ɗin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262