Arewa
Yan ta'addan Boko Haram sun kai hari da motocin yaki, suna kona gine-gine da motoci inda suka hallaka kwamandan sojoji tare da jikkata wasu a jihar Borno.
Bayan suka daga gwamnatin jihar Kano, rundunar 'yan sandan Kano ta janye matakin hana Mauludin Tijjaniyya bayan ta yi zargin kai harin ta'addanci.
Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya kai ziyara Bauchi domin halartar babban taro inda ya nuna godiya ga Sarkin Bauchi da majalisarsa kan addu'o'i.
Masana sun gargadi mutane yayin da aka gano ana sayar da gurbataccen manja mai lahani a kasuwannin Najeriya. Hukumar NAFDAC ta tabbatar da hakan.
Gwamnonin arewa sun yi ta'aziyyar marigayi Lt. Gen. Useni, jajirtaccen gwarzo mai kishin kasa wanda ya rasu yana da shekaru 82 bayan fama da doguwar jinya.
Gwamnatin Tarayya ta ayyana kungiyar Lakurawa a matsayin ta ta'addanci tare da haramta ta da sauran kungiyoyin da ke da alaka da ita a Arewacin Najeriya.
Farashin kayan hatsi a kasuwar Dandume da ke jihar Katsina ya karye sosai, shinkafa N55,000, wake N90,000, gero N67,000; yayin da kasuwar ke ci sau uku a sati.
Rahotanni sun tabbatar da cewa tankar mai ta sake faduwa a jihar Taraba inda matasa suka taru a wurin yayin da jami'an tsaro suka dakatar da su daga diban fetur.
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya tabbatar da bin doka inda ya mayar da basarake, Jonathan Paragua Zamuna matsayin sarkin Piriga bayan Nasir El-Rufai ya tube shi.
Arewa
Samu kari