Kwana Ya Kare: Mahaifiyar Sarki da Shugaban Karamar Hukuma a Borno Ta Rasu
- Mahaifiyar Sarkin Gwoza, Hajiya Asta Shehu Timta, ta rasu bayan ta shafe fiye da shekaru 80 a duniya tana hidima ga al’umma
- Hajiya Asta ita ce mahaifiyar shugaban ƙaramar hukumar Gwoza, Yarima Abba Kawu Shehu Timta
- Masarautar Gwoza ta tabbatar da mutuwar inda aka ce an gudanar da jana’izar Hajiya Asta a ranar Asabar bayan sallar azahar a fadar Sarkin Gwoza
- Wani mazaunin Askira, Alhaji Umar Mai Hula ya shaidawa wakilin Legit Hausa cewa marigayiyar ta rasu ne tun ranar Juma'a da dare
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Maiduguri, Borno - Allah ya karbi rayuwar, Hajiya Asta Shehu Timta, mahaifiyar Sarkin Gwoza, Alhaji Muhammadu Shehu Idrisa Timta.
Rahotanni sun tabbatar da cewa marigayiyar ta rasu a ranar Juma'a kamar yadda wata sanarwa daga Masarautar Gwoza ta tabbatar.

Asali: Original
Masarautar Gwoza ta sanar da rasuwar mahaifiyar Sarki
Sanarwar ta bayyana cewa Hajiya Asta ta rasu ne a yammacin Juma'a 14 ga watan Maris, 2025, cewar Aminiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tabbatar marigayiyar ta rasu tana da shekaru sama da 80 da haihuwa kafin ta bar duniya.
Kazalika, Hajiya Asta ita ce mahaifiyar Yarima Abba Kawu Shehu Timta, wanda ke matsayin Shugaban Ƙaramar Hukumar Gwoza a jihar Borno.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an yi sallar jana’izarta a ranar Asabar bayan sallar azahar a fadar Sarkin Gwoza da ke cikin karamar hukumar.
A cewar masarautar:
“Hajiya Asta ta kasance tsohuwar malamar makaranta da ta bayar da gagarumar gudummawa wajen bunkasa ilimi a Gwoza.”

Asali: Facebook
Gudunmawar da marigayiyar ta ba al'umma
Rahoton ya bayyana cewa, har zuwa rasuwarta, Hajiya Asta tana ci gaba da tallafa wa harkokin ilimi da kuma taimaka wa al’umma.
Masarautar Gwoza ta bayyana mutuwarta da cewa:
“Rasuwarta babban gibi ne da ba za a iya cikewa cikin sauki ba.”
’Yan uwa da al’ummar Gwoza sun bayyana jimami da alhini, inda suka ce Hajiya Asta uwa ce ga kowa, ba wai ga danginta kaɗai ba.
Legit Hausa ta yi magana da wani mazaunin Askira
Alhaji Umar Mai Hula Askira ya shaidawa wakilin Legit Hausa cewa marigayiyar ta rasu ne tun ranar Juma'a da dare.
Mai Hula Askira ya ce sun samu halartar sallar jana'izar tare da Sarkin Askira a ranar Asabar 15 ga watan Maris, 2025.
"Jiya mu muka je jana'izar marigayiyar tare muka tafi da Sarkin Askira saboda mun bar Askira da safe kamar karfe shida sai daf mangariba muka dawo gida."
- Cewar Alhaji Umar Mai Hula Askira
Farfesa a Jami'ar ABU ya kwanta dama
Kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya nuna alhinin rasuwar Farfesa Kharisu Chukkol, fitaccen masanin shari’a daga jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan
Mutuwa mai yankar ƙauna: Tsohon ɗan Majalisa ya rasu kwanaki 7 kafin bikin ƙarin shekara
Marigayin ya riƙe mukamai da dama a ABU, ciki har da shugaban sashen koyar da shari’a da kuma daraktan cibiyar harkokin gudanarwa.
Shugaban ƙasa ya yaba da gudunmawar da Farfesa Chukkol ya bayar, musamman littafinsa na 1988 mai take: "Dokar Laifuffuka a Najeriya".
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng