Tsaro Ya Fara Samuwa, Hare Haren Yan Ta'adda Sun Ragu da Fiye da 70% a Najeriya

Tsaro Ya Fara Samuwa, Hare Haren Yan Ta'adda Sun Ragu da Fiye da 70% a Najeriya

  • Hedikwatar Tsaro ta ce yawan hare-haren da yan ta'adda ne kai wa ya ragu da kashi 73.3% a watan Oktoban 2026
  • Alkaluma sun nuna cewa an samu hare-hare 98 a watan Oktoba, sabanin 367 da aka samu a watan Satumban da ya gabata a 2026
  • Duk da raguwar hare-haren, sojoji sun kashe sama da ’yan ta’adda 217, tare da kuɓutar da mutum 349 da aka yi garkuwa da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja – Hedikwatar Tsaro ta Ƙasa (DHQ) ta ce yawan hare-haren da aka kai a wuraren da sojojin Najeriya ke gudanar da ayyuka a faɗin ƙasar nan ya ragu da kashi 73.3% a watan Oktoban 2026.

Daraktan Yaɗa Labarai na Ayyukan Tsaro, Manjo Janar Michael Onoja, ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Juma'a yayin da yake ba da bayanin ayyukan sojoji a sassa daban-daban na ƙasar.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Dakarun sojojin Najeriya sun tura yan ta'adda sama da 200 lahira

Oluyede.
Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Olufemi Oluyede Hoto: @DHQNigeria
Source: Twitter

A cewarsa, an samu hare-hare 98 a watan Oktoba, idan aka kwatanta da hare-hare 367 da aka samu a watan Satumba, 2026, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.

A cewarsa, an samu hare-hare 98 a watan Oktoba, wanda ya yi kasa sosai idan aka kwatanta da hare-hare 367 da aka samu a watan Satumba, 2026, cewar tashar Channels tv.

Ya ce hakan na nufin an samu raguwar hare-hare 269 cikin wata guda, inda ya danganta nasarar da aka samu da ci gaba da ƙoƙarin da dakarun soji ke yi a wuraren ayyukana wanzar da zaman lafiya daban-daban.

Yankunan da aka fi kai hare-hare

Bayanan watan Oktoba sun nuna cewa rundunar soji ta Operation Enduring Peace ce ta fi samun hare-hare, inda aka kai hare-hare 29 a yankin da take aiki

Operation Hadin Kai ta biyo baya da hare-hare 27, yayin da Operation Fansan Yamma ta samu hare-hare 24.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace dan takarar shugaban kasa a Najeriya

Operation Whirl Stroke ta samu hare-hare 12, yayin da Operation Udo Ka ta samu hare-hare huɗu.

Haka kuma, Operation Delta Safe da Operation Savannah Shield kowannensu ya samu hari guda ɗaya kacal a watan Oktoba, 2026, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Hafsan tsaron Najeriya ya ja hankali

Onoja ya ce Babban Hafsan Tsaro, Janar Olufemi Oluyede, ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa rundunar soji za ta ƙara ƙaimi wajen kamo waɗanda ke da hannu a hare-haren tare da gurfanar da su gaban shari'a.

Ya kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su ƙara ƙarfafa musayar bayanan sirri da tsara ayyuka tare.

Dakarun soji.
Dakarun rundunar sojojin Najeriya a bakin aiki Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Twitter

Haka zalika, ya buƙaci shugabannin al’umma da mazauna yankuna su riƙa sanar da jami'an tsaro duk wani abu da suka gani mai tayar da hankali, ta hanyar tuntuɓar cibiyar tsaro mafi kusa ko kuma layin rundunar soji na kyauta mai lamba 193.

Sojoji sun kashe yan ta'adda 217

Kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun kashe ’yan ta’adda 217 tare da kama mutum 333 da ake zargi da ta’addanci a watan Oktoba 2026.

Dakarun sojin sun kuma kuɓutar da mutane 349 da aka yi garkuwa da su a sassa daban-daban na ƙasar nan a watan Oktoba na shekarar 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262