'Yan Bindiga Sun Sace Dan Takarar Shugaban Kasa a Najeriya

'Yan Bindiga Sun Sace Dan Takarar Shugaban Kasa a Najeriya

  • Rahotanni sun nuna cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kai farmaki wajen cin abinci da dan takarar shugaban kasa na AAC, Omoyele Sowore ya je
  • Bayanan da Legit Hausa ta samu sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a wajen wani cin abinci da ke Ado-Ekiti da ranar Juma'a, 30 ga Oktoba
  • Jama'a da dama sun fara kira ga jami'an tsaro su gaggauta kubutar da dan takarar shugaban kasar duk da har yanzu ba a san wadanda suka sace shi ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Ekiti - Rahotanni da ke fitowa sun nuna cewa dan takarar shugaban kasa na AAC, Omoyele Sowore ya fada hannun masu garkuwa da mutane dauke da makamai.

Hakan na zuwa ne bayan farmaki da wasu da ake kyautata zaton 'yan bindiga ne suka kai masa da ranar Juma'a, 30 da Oktoban 2026.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun sake auka wa Kaduna, sun kuma yin garkuwa da bayin Allah

Omoyele Sowore
Omoyele Sowore da aka sace. Hoto: Omoyele Sowore
Source: Facebook

Legit ta samo bayanai game a kai farmakin ne a wasu jerin sakonni da dan takarar shugaban kasar ya wallafa a shafinsa na Facebook.

An sace Sowore a Ekiti

Rahotonni sun nuna cewa an kai wa Omoyele Sowore da tawagar shi hari ne a wani wajen cin abinci da ke Ado Ekiti.

Ga wasu sakonnin da aka wallafa a shafinsa na Facebook:

"’Yan daba sun kai mana hari a cikin wani gidan abinci a Ado Ekiti."

Biyo bayan haka, an sake wallafa cewa:

"’Yan daba dauke da makamai sun yi garkuwa da Sowore. Ba a san inda yake a yanzu ba."

Lauya ya yi kira ga 'yan sanda

Lauya mai fafutukar kare hakkin dan adam, Inibehe Effiong ya yi kira ga jami'an tsaro da su gaggauta ceto Omoyele Sowore.

A sakon da ya wallafa a Facebook, lauyan ya ce:

“Na shiga damuwa matuƙa da labarin sace ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, da wasu mutane ɗauke da makamai da har yanzu ba a gano ko su waye ba a jihar Ekiti.

Kara karanta wannan

Amurka ta kawo ɗauki mai zafi, manyan 'yan ta'adda sun fara guduwa a Najeriya

Mutanen ɗauke da makaman sun kai wa Sowore hari tare da magoya bayansa.
Ya kamata Sufeto-Janar na ’Yan Sanda ya ɗauki matakan gaggawa da tsauri domin tabbatar da tsaron Sowore da kuma kuɓutar da shi.
Sowore bai taɓa amfani da tashin hankali wajen fafutukar neman inganta Najeriya ba. Sai dai, babu wanda ya mallaki tashin hankali shi kaɗai.
Rundunar ’Yan Sandan Najeriya da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (SSS) dole ne su ɗauki matakin gaggawa kan wannan lamari.”

An sace mai ciki Kaduna

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu 'yan bindiga masu garkuwa da mutane sun sace wata mata mai juna biyu a jihar Kaduna mako uku da suka wuce.

Rahotanni sun nuna cewa yayin da suka kira iyalan matar domin su tabbatar da cewa tana raye, matar mai suna Jamila ta ce cikinta ya zube.

Biyo bayan haka, jama'a da dama da suka hada da 'yan uwa da abokan arziki sun nuna damuwa tare da kira ga jami'an tsaro sun ceto ta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng