"Manufofinsa Na Amfanar Kowa," Tanko Yakasai Ya Nemi Arewa Ta Mara wa Tinubu Baya

"Manufofinsa Na Amfanar Kowa," Tanko Yakasai Ya Nemi Arewa Ta Mara wa Tinubu Baya

  • Dattijon dan siyasa, Tanko Yakasai ya jaddada goyon bayansa ga gwamnatin shugaba Bola Tinubu saboda kyawawan manufofinsa ga Arewa
  • Yakasai ya ce rahotanni sun nuna cewa farashin kayan masarufi da man fetur na sauka, lamarin da ke rage wa 'yan Najeriya radadin tattalin arziki
  • Ya kara da cewa saboda haka, akwai bukatar mazauna shiyyar su kara mara wa gwamnatin tarayya baya domin akwai manufofi masu kyau a gaba
  • Yakasai ya jaddada cewa akwai wasu muhimman maufofi a nan gaba, wanda gwamnati ta ba da tabbacin za su amfani baki daya 'yan Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Dattijo kuma ɗan siyasa a jamhuriyar farko, Alhaji Tanko Yakasai, ya nuna goyon bayansa ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

An yi ca kan NYSC bayan barazana ga mai bautar ƙasa da ta soki gwamnatin Tinubu

Ya kara da cewa gwamnati mai ci a yanzu ta na samar da manufofin da ke kawo nasarori da dama, musamman a fannin tattalin arziki.

Yakasai
Yakasai ya ce manufofin Tinubu su na aiki Hoto: Salihu Tanko Yakasai/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa dattijon ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke gana wa da manema labarai a Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alhaji Tanko Yakasai ya yaba wa ‘yan Najeriya bisa goyon bayansu da addu’o’in da suke yi wa Tinubu don nasara.

Dalilan Tanko Yakasai na yabon gwamnatin Tinubu

Jaridar This day ta wallafa cewa Alhaji Tanko Yakasai na ganin manufofin da gwamnatin tarayya ta bijiro da su sun fara haifar da 'da mai ido.

Ya ce:

"Ina samun rahotanni cewa farashin kayan abinci na raguwa akai-akai. Ba kamar da ba, yanzu iyalai na iya samun kayan masarufi kamar shinkafa, wake, masara da dawa."
"Haka kuma, na samu bayanai cewa farashin man fetur ya ragu, inda wasu gidajen mai ke sayarwa a kan N850 kowace lita, maimakon N1,150 da ake siyarwa a baya.

Kara karanta wannan

Albarkacin azumi: Yadda almajirai suka yi cudanya da gwamnan Nasarawa

Wannan na da muhimmanci ga harkokin sufuri da walwalar ‘yan Najeriya."

Yakasai ya nemi a tallafawa Tinubu

Yakasai, wanda ya kasance babban mai mara wa Bola Tinubu baya a zaɓen 2023, ya yi kira ga ‘yan Arewa da su ci gaba da goyon bayan gwamnati.

Ya jaddada cewa gwamatin, karkashin Bola Tinubu ba ta ware Arewa daga cikin kyawawan manufofin da za su inganta rayuwar mazauna shiyyar ba.

Tinubu
Yakasai na ganin akwai wasu manufofi masu kyau da Tinubu ya shirya wa Najeriya Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ya kuma tabbatar da cewa akwai ƙarin manufofi da shirye-shirye na ci gaba da za su amfanar da ‘yan Najeriya, musamman mutanen Arewa.

Yakasai ya bukaci ‘yan siyasa da al’umma su bada gudunmawa wajen inganta dimokuraɗiyya ta hanyar suka masu fahimta da tattaunawa mai amfani.

Gwamnatin Tinubu ta juya wa majalisa baya

A wani labarin, mun wallafa cewa gwamnatin tarayya ta nuna rashin amincewarta da kudirin majalisar tarayya na kafa sababbin jami’o’i kusan 200 a sassa daban daban na Najeriya.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Shugaban Amurka, Trump ya samu izinin kakaba takunkumi ga Najeriya

Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ya bayyana cewa Najeriya na da jami’o’i 278, ciki har da 64 mallakin tarayya, 67 na jihohi, sannan 147 na masu zaman kansu masu fama da kalubale.

Najeriya na da jami’o’i 278, ciki har da 64 mallakin tarayya, 67 na jihohi, sannan 147 na masu zaman kansu, wanda Alausa ke ganin inganta su zai fi a maimakon gina sababbi a kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng