Zargin N240m: Kotu Ta Umarci Kama Kwamishinan Ganduje, An Jero Laifuffuka

Zargin N240m: Kotu Ta Umarci Kama Kwamishinan Ganduje, An Jero Laifuffuka

  • Babbar Kotun Jihar Kano ta ba da umarnin kama tsohon Antoni-Janar kuma Kwamishinan Shari'a, M. A. Lawal, bisa zargin ɓatar N240m
  • Baristan yana fuskantar tuhume-tuhume huɗu da suka shafi ɓatar da kuɗi da cin amana, an aike masa da sammaci, amma ya gaza zuwa kotu
  • Alƙalin kotun jihar Kano, Mai Shari'a Amina Adamu Aliyu, ta bayar da umarnin kama Lawal tare da ɗage shari'ar zuwa 6 ga Mayun 2025
  • A wata shari'a daban, kotun ta bayar da umarnin kama tsohon shugaban hukumar KSIP, Jibrilla Muhammad, bisa zargin ɓatar N212m a ofis

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Babbar Kotun Jihar Kano ta bayar da umarnin kama tsohon Kwamishinan Shari'a a gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje kan wasu zarge-zarge da ake yi masa.

Kotun ta bukaci cafke Barista M. A. Lawal, bayan ya gaza bayyana a kotu kan tuhume-tuhume da ake masa da suka hada da batar da makudan kudi har N240m.

Kara karanta wannan

Magajin Rafi: Dattijon Arewa ya yi murabus, Masarautar Zazzau ta yi sabon nadi

Kotu ta bayar da umarni kan zargin badakala kan kwamishinan Ganduje
Ana zargin kwamishinan Ganduje da batar da N240m. Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Asali: Facebook

Tsohon shugaban hukumar KSIP ya shiga matsala

Leadership Hausa ta ce ana tuhumar Lawal da laifuffuka huɗu masu alaƙa da ɓatar da kuɗi da cin amana da suka kai N240m.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wata shari'a daban, kotun ta bayar da umarnin kama Jibrilla Muhammad, tsohon shugaban hukumar na Zuba Jari da Kadarorin Kano (KSIP).

An ba da umurnin ne bisa zargin ɓatar da makudan kudi har N212m da ake tuhumar tsohon shugaban kamfanin da karkatarwa a lokacin da yake jan ragamar shugabancinsu.

An ɗage shari'ar ta su zuwa 29 ga Afrilun 2025, bayan abokin shari'arsa, Dauda Sheshe, bai karɓi sammaci ba.

An umarci kama tsohon kwamishinan Ganduje a Kano
Kotu ta umarci kama kwamishinan Ganduje kan zargin badakalar N240m. Hoto: All Progressives Congress.
Asali: Twitter

An aike da sammaci ga kwamishinan Ganduje

Shari'ar tsohon kwamishinan shari'a a Kano ta shafi Abdullahi Umar Ganduje, shugaban jam'iyyar APC na ƙasa kuma tsohon gwamnan jihar.

A zaman kotun na Litinin 17 ga watan Maris, 2025 masu gabatar da ƙara sun sanar da kotu cewa har yanzu ba a miƙa wa Ganduje sammaci ba, duk da umarnin da aka bayar a baya.

Kara karanta wannan

An karrama Buhari tare da manyan malamai da 'yan siyasar Najeriya

Kotun ta ce duk da an aike wa tsohon kwamishinan a gwamnatin Abdullahi Ganduje sammaci, bai bayyana a gare ta ba wanda hakan ya tilasta fitar da wannan umarni.

Alƙalin kotun, Mai Shari'a Amina Adamu Aliyu, ta bayar da umarnin kama Lawal tare da ɗage shari'ar zuwa 6 ga Mayun 2025 da muke ciki, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.

An yabawa salon shugabancin Ganduje

Mun ba ku labarin cewa sabon shugaban hukumar raya kogin Hadejia da Jama’are, Rabiu Suleiman Bichi, ya bayyana cewa Kano za ta kada kuri'a sosai ga APC.

'Dan siyasar ya godewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu bisa nadin Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar ta ƙasa, ya ce hakan ba karamin abin alfahari ba ne.

Bichi ya soki gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta NNPP, har yake cewa manufofinta sun sa mutane sun daina sha'awar jam'iyyar tun kafin zaben shekarar 2027.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng