Arewa
Rahotanni daga garin Kano sun nuna cewa wata mummunar gobara da ta tashi da tsakar dare ta ƙone shaguna akalla 19 da wani Masallaci a kaauwar Rimi, cikin Kano.
Yan kasuwar hatsi a kasuwanin babban birnin tarayya Abuja sun ce ba su karbar tiransifa sai dai tsabar kudi saboda suma a wurin manoman kauye suka siyo hatsi.
Hukumar tsaro ta NSCDC a jihar Jigawa ta ce ta gano wani mutum a sume a gefen titi da kebur a wuyarsa wanda daga bisani aka gano an masa fashin N97,000 a tasi.
Kotun kolin Najeriya ya yanke hukunci da cewa, ya amince da takarar Dauda Lawal Dare a matsayin sahihin dan takarar da zai gwabza a zaben gwamnan PDP mai adawa.
Rahotannin da muka samu daga kauyen Maigari, ƙaramar hukumar Rimin Gado a jihar Kano sun nuna cewa wasu maharan sun harbe magajin gari har lahira da daddare.
Rahotanni daga arewa maso gabashin Najeriya sun nuna cewa akalla mayakan Boko Haram 1,250 suka miƙa wuya ga rundunar sojin Najeriya cikin kwanaki Bakwai 7.
Yan bindiga sun halaka wani mutum dan shekara 52 mai suna Samanja a garin garin Baje-Patiko da ke karamar hukumar Manya ta jihar Neja yayin da ya ke aiki a gona
Mummunan gobara ta tashi a kasuwar Kurmi da ke birnin Kano a ranar Laraba 1 ga watan Maris inda kimanin shaguna 80 suka kone kuma aka tafka asarar miliyoyi.
Ibrahim Dankwambo, tsohon gwamnan jihar Gombe yayi nasara ya lashe zaben sanata na mazabar Gombe Central North da kuri'u 143155 inda ya kada Alkali na APC 77948
Arewa
Samu kari