An Gurfanar Da Wani Matashi a Gaban Kotun Shari'ar Musulunci Bisa Zargin Sace Lasifikar Masallaci a Kano

An Gurfanar Da Wani Matashi a Gaban Kotun Shari'ar Musulunci Bisa Zargin Sace Lasifikar Masallaci a Kano

  • An gurfanar da wani matashi a gaban kotu bayan ya shiga har cikin masallaci a jihar Kano ya tafka mummunar sata
  • Matashin ya sace lasifika da wayar kebur na masallacin Usman Ibn-Affan da ke a birnin Kano wanda kuɗinsu ya kai N70,000
  • Matashin wanda aka gurfanar a gaban kotun shari'ar musulunci, ya musanta aikata laifin da ake tuhumarsa da shi

Jihar Kano - An gurfanar da wani matashi mai shekara 20 a gaban kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a birnin Kano, bisa zargin aikata laifin satar lasifikar masallaci.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa matashin mai suna Halifa Sani, wanda ya ke a Gadon Kaya cikin birnin Kano, an gurfanar da shi a gaban kotun ne ranar Laraba, 7 ga watan Yunin 2023.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-ɗumi: Hawaye Sun Kwaranya Yayin Da Sanatan Najeriya Mai Karfin Fada A Ji Ya Rasu A Asibitin Amurka

Matashi ya gurfana kotu kan satar lasifikar masallaci a Kano
A na zargin matashin da aikata laifin sata a masallaci Hoto: Gazettngr.com
Asali: UGC

A na zargin matashin ne dai da shiga cikin masallacin Usman Ibn-Affan da sace sifikar masallacin da kuma wayar kebur waɗanda kuɗinsu sun kai N70,000.

An kai rahoton wannan aika-aikar da matashin ya aikata ne a ofishin ƴan sanda a ranar 2 ga watan Yunin 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mai shigar da ƙara, jami'in ɗan sanda mai matsayin sufeta, Abdullahi Wada, ya bayyana cewa wani Malam Nura Mohammed shine ya kai ƙorafin satar da matashin ya yi a gaban ƴan sanda.

Abdullahi ya bayyana cewa Malam Nura ya shigar da ƙorafin ne a ofishin ƴan sanda na Gwale cikin birnin Kano a ranar 2 ga watan Yunin 2023.

Ya yi satar da kuɗinta sun kai N70,000

Mai shigar da ƙarar ya bayyana cewa wanda ake ƙarar ya sace lasifika ta masallacin Usman Ibn-Affan wacce kuɗinta sun kai N50,000 da wayar kebur wacce kuɗinta sun kai N20,000.

Kara karanta wannan

Kwanaki 9 da Barin Kujerarsa, Ministan Buhari Ya Sake Samun Wani Aiki Mai Tsoka

Sai dai wanda ake ƙarar bisa zargin tafka sata a masallaci ya musanta aikata laifin da ake tuhumarsa da shi a gaban kotun, cewar rahoton The Guardian.

Alƙalin kotun, mai shari'a Malam Umar Lawal-Abubakar, ya bayar da belinsa kan kuɗi N10,000 da sharaɗin dole sai wani mutum ɗaya ya tsaya masa wanda ya ke ɗan'uwansa na jini.

Alƙalin ya kuma ɗage sauraron ƙarar har sai zuwa ranar 22 ga watan Yuni domin ci gaba da shari'ar.

Magidanci Mai Mata Biyar Ya Gurfana a Kotu

A wani labarin na daban kuma an gurfanar da wani magidanci mai auren mata biyar a gaban wata kotun shari'ar musulunci a Kaduna.

Ana zargin magidancin da ya auren mata biyar wanda hakan ya saɓawa koyarwar addinin musulunci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel