Gwamnonin Arewa Ta Yamma Ba Zasu Sake Bai Wa Yan Bindiga Kuɗi Ba, Uba Sani

Gwamnonin Arewa Ta Yamma Ba Zasu Sake Bai Wa Yan Bindiga Kuɗi Ba, Uba Sani

  • Gwamnan Kaduna ya ce shi da sauran gwamnonin jihohin Arewa ta Yamma sun cimma matsaya kan hanyar da zasu tunkari matsalar tsaro
  • Malam Uba Sani ya ce sun yanke cewa ba zasu bi hanyar da wasu tsofafin gwamnoni suka bi na bai wa yan bindiga kudi ba
  • A cewarsa, sun shirya zuwa su gana da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, kan rashin tsaron da ya addabi jihohinsu

Kaduna - Gwamna Malam Uba Sani na jihar Kaduna, ranar Talata, ya ce shi da sauran gwamnonin Arewa maso Yamma sun zauna sun yanke cewa ba zasu bi hanyar bai wa yan bindiga kuɗi ba.

Uba Sani ya ce a halin yanzun gwamnatinsa zata maida hankalin wajen aikin raya karkara a matayin hanya ɗaya tilo ta bunƙasa rayuwar mutanen ƙauye da nufin magance matsalar tsaro a jihar.

Kara karanta wannan

Gwamna Uba Sani Ya Tona Asirin Wasu Gwamnoni da Suka Rika Ma'amala da Yan Ta'adda a Jihohinsu

Malam Uba Sani.
Gwamnonin Arewa Ta Yamma Ba Zasu Sake Bai Wa Yan Bindiga Kuɗi Ba, Uba Sani Hoto: Sen Uba Sani
Asali: Facebook

Gwamna Sani ya yi wannan furucin ne yayin hira da kafar Channels tv a cikin shirinsu na Sunrise Daily ranar Talata, 6 ga watan Yuni, 2023.

Haka nan kuma Gwamnan Kaduna ya ƙara da cewa gwamnonin shiyyar Arewa ta Yamma sun cimma matsayar cewa zasu tunkari shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu kan kalubalen tsaron da ya addabi yankinsu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jaridar Punch ta tattaro cewa a kalamansa, gwamna Uba Sani ya ce:

"Na haɗa taron gwamnonin shiyyar Arewa maso yamma da gwamnan jihar Neja, inda muka zauna muka fitar da hanyar magance matsalar tsaron da ta addabi jihohin mu."
"Mun amince zamu haɗa kai mu yi aiki tare kuma zamu kaucewa matakin da gwamnatocin tsoffin gwamnoni suka ɗauka na bai wa 'yan ta'adda kuɗaɗe."
"Haka nan muna shirye-shiryen zuwa mu gana da mai girma shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalar tsaro."

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Gana da Shugabannin Tsaro Bayan Yan Bindiga Sun Kashe Rayuka 37, Ya Ɗauki Matakai Masu Kyau

Dangane da batun cire tallafin Man fetur, gwamna Sani ya ce ya gana da wakilan ƙungiyoyin kwadago kuma sun amince zasu haɗa hannu da gwamnati a yi aiki tare.

Gwamna Aliyu Ya Tallafawa Mutanen da Harin Yan Bindiga Ya Shafa a Sakkwato

A wani labarin kuma Gwamna Ahmad Aliyu na Sakkwato ya ziyarci garuruwan da yan bindiga suka kai harin rashin imani ranar Asabar, ya tallafa musu da kuɗaɗe da abinci.

Gwamna Aliyu ya baiwa iyalan tallafin kuɗi da kuma kayan abinci. Haka nan waɗanda suka ji raunuka da asarar dukiya a harin ya basu tallafin kuɗi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel