Mummunar Gobara Ta Tashi a Wata Babbar Kasuwa a Jihar Yobe, An Tafka Gagarumar Asara

Mummunar Gobara Ta Tashi a Wata Babbar Kasuwa a Jihar Yobe, An Tafka Gagarumar Asara

  • Wata mummunar gobara da ta tashi ta ritsa da ƴan kasuwa da dama a wata babbar kasuwa a birnin Damaturu na jihar Yobe
  • Gobarar wacce ta tashi cikin dare ta kwashe sa'o'i da dama kafin a kashe ta inda ta janyo asarar dukiya mai yawa
  • Gwamnatin jihar Yobe ta yi alƙawarin ba ƴan kasuwar da gobarar ta ritsa da su tallafin domin rage asarar da suka tafka

Jihar Yobe - Ƴan kasuwa sun tafka asara bayan mummunar gobara ta tashi a kasuwar Bayan-Tasha, cikin birnin Damaturu, babban birnin jihar Yobe.

Jaridar Punch ta kawo rahoto cewa gobarar ta laƙume kayayyaki da dama bayan ta tashi a kasuwar.

Gobara ta tashi a kasuwar Bayan-tasha a Damaturu
Gobara a kasuwa (ba inda lamarin ya auku ba) Hoto: Ripplesnigeria.com
Asali: UGC

Gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe 1:00 na dare a ranar Juma'a inda ba a samu nasarar kashe ta ba har sai wajen ƙarfe 4:00 na dare.

Wani mai suna Babannan Garba, wanda ya bayyana takaicinsa kan gobarar a shafinsa na Facebook, ya bayyana cewa kayayyaki na miliyoyin naira suka lalace a dalilin gobarar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hotuna da dama da aka sanya a soshiyal midiya sun nuna ƴan kasuwar na ƙoƙarin kwaso ragowar abinda ya rage a cikin gobarar.

Gwamnati za ta bayar da tallafi ga ƴan kasuwar

A yayin da ya ke aikewa da saƙon jaje kan waɗanda gobarar ta ritsa da su, gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, a cikin wata sanarwa ta hannun hadiminsa, Mamman Mohammed, ya ce gwammnati za ta kawo agaji.

"Gwamnati za ta yi duba kan wannan gagarumar asarar da aka yi domin bayar da agaji ga waɗanda lamarin ya ritsa da su domin su farfaɗo su dawo kan harkokin kasuwancinsu." A cewarsa.

"Nan bada daɗewa ba za a ba ƴan kasuwa sabbin kasuwannin zamani na Damaturu, Gashua da Nguru domin komawa cikin muhalli wanda ya ke da tsaro, domin kare su daga iftila'in yawan tashin gobara a kasuwanni.
"Sabbin kasuwannin da aka ƙaddamar an ginasu ne da fasahar maganin gobara ta hanyar amfani da ƙonannun bululluka domin kare kayayyaki daga tashin gobara."

Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani mazaunin birnin Damaturu wanda ya samu halartar inda gobarar ta tashi a kasuwar ta Bayan-Tasha.

Musa Malami ya bayyana cewa gobarar ta tashi ne a ɓangaren masu sana'ar yadi na kasuwar inda ta lamushe shaguna 25, waɗanda suka ƙone ƙurmus wanda hakan ya janyo aka tafka asarar miliyoyin naira.

Ya yi bayanin cewa a bayanan da ya samu bayan ya je kasuwar, gobarar ta tashi ne a dalilin wutar lantarki.

Gobara Ta Tashi a Fitacciyar Kasuwar Agbeni Da Ke Jihar Oyo

A wani labarin na daban kuma, kun ji yadda wata mummunar gobara ta tashi a fitacciyar kasuwar Agbeni da ke a birnin Ibadan na jihar Oyo.

Gobarar wacce ta tashi cikin tsakar dare ta ƙone shagunan ƴan kasuwa da dama inda ta janyo mummunar asara ta miliyoyin naira.

Asali: Legit.ng

Online view pixel