Wasu Bata-Gari Sun Bankawa Gidan Rediyon Jihar Kogi Wuta

Wasu Bata-Gari Sun Bankawa Gidan Rediyon Jihar Kogi Wuta

  • Ɓata-gari sun aikata mummunar ta'asa a jihar Kogi bayan sun bankawa gidan rediyon jihar wuta da sace muhimman kayayyaki
  • Miyagun ɓata-garin sun kuma sace dukkanin wasu muhimman kayan aiki da ke a gidan rediyon bayan sun lakadawa masu gadi dukan tsiya
  • Gwamnatin jihar ta sha alwashin yin bakin ƙoƙarinta wajen ganin an cafko su tare da gurfanar da su gaban hukuma

Jihar Kogi - Wasu ɓata-gari sun farmaki gidan tashar gidan rediyon jihar Kogi da safiyar ranar Talata, rahoton Aminiya ya tabbatar.

Ɓata-garin sun ƙona gidan rediyan na Kogi Radio 90.5 FM da ke a Ochaja cikin ƙaramar hukuma Dekina, inda suka sace kayayyakin da ke a cikinsa.

Bata-gari sun kona gidan rediyon jihar Kogi
Bata-garin sun kuma sace muhimman kayayyakin aiki Hoto: Punch.com
Asali: UGC

Masu gadin tashar gidan rediyon sun sha na jaki a hannun ɓata-garin waɗanda suka ƙona dukkanin wasu muhimman kayayyakin aiki da ke a gidan rediyon.

Kara karanta wannan

Wasu Manyan Jiga-Jigan PDP da Ɗumbin Mambobi Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC a Arewa

Wani shaida ya bayyana cewa ɓata-garin sai da suka bi suka sace duk wani muhimmin kayan aiki a tashar gidan rediyon.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa har wani janareto ƙirar Mikano da ɗaya daga cikin ƴan takarar gwamnan jihar ya bayar bai tsira ba daga hannun ɓata-garin inda suka yi awon gaba da shi, cewar rahoton Tribune.

Gwamnatin jihar ta yi Allah wadai da harin

A cikin wata sanarwa da kakakin ma'aikatar ƴada labarai ta jihar, Salawu Patience, ta fitar ta bayyana cewa gwamnatin jihar ta yi Allah wadai da wannan aikin ta'asar, inda ta bayar da tabbacin cewa jami'an tsaro na aiki tuƙuru domin cafke ɓata-garin.

Kakakin ta bayyana cewa kwamishinan ma'aikatar Kingsley Fanwo, tare da darakta-janar na hukumar yada labaran jihar, Alhaji Ojo Oyila Ozovehe, sun kai ziyara gidan rediyon domin ganewa idanunsu irin aika-aikar da aka tafka a wajen.

Kara karanta wannan

Shugabancin Majalisa: Cikakkun Bayanai Kan Ziyarar Yari Wajen Buhari a Daura Sun Bayyana

Shirye-shirye sun tsaya cak a tashar bayan an kulleta saboda ɓarnar da aka yi amma gwamnatin na yin duk mai yiwuwa wajen ganin an ci gaba da aiki a tashar ba tare da ɓata wani dogon lokaci ba.

Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP William Aya, ya ci tura saboda bai amsa kiran wayarsa ba da saƙon da aka tura masa a waya.

Yan Daba Sun Farmaki Ayarin Motocin Yahaya Bello

A wani rahoton na daban kuma, ƴan daba sun farmaki kwamban motocin gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello.

Ƴan daban waɗanda ake kyautata zaton na siyasa ne sun farmaki gwamnan ne akan hanyarsa ta zuwa Lokoja daga birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel