Rikicin Shugabanci: Fusatattun Matasa Sun Fara Zanga-Zanga a Harabar Majalisa, Sun Fadi Dalilinsu

Rikicin Shugabanci: Fusatattun Matasa Sun Fara Zanga-Zanga a Harabar Majalisa, Sun Fadi Dalilinsu

  • Matasa sun fara zanga-zanga a harabar majalisar jihar Nasarawa saboda dakatar da kaddamar da majalisar da gwamnan ya yi
  • Matasan suna zargin gwamnan da kakaba wa mutane shugabannin majalisar wadanda mutane ba sa goyon baya a majalisar
  • Magatakardan majalisar, Ibrahim Musa, a wata sanarwa ya bayyana dage kaddamar da majalisar ta bakwai saboda dalilai na tsaro

Jihar Nasarawa – Wasu fusatattun matasa sun fara zanga-zanga a Lafia babban birnin jihar Nasarawa don nuna rashin jin dadinsu game da dakatar da kaddamar da majalisar jihar ta bakwai.

Wannan na zuwa ne bayan gwamnan jihar, Abdullahi Sule ya dakatar da kaddamar da majalisar saboda barazanar rashin tsaro da aka samu.

Majalisar jihar Nasarawa
Rikicin Shugabanci: Fusatattun Matasa Sun Fara Zanga-Zanga a Harabar Majalisa. Hoto: Daily Post.
Asali: Facebook

Daily Trust ta tattaro cewa da misalin karfe 5 na safiyar Talata 6 ga watan Yuni, jami’an tsaron hadin gwiwa sun bazama a wurare da dama don tabbatar da samun doka da dakile tashin hankali.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Mambobi Majalisa Sun Zabi Kakakin Majalisar Dokoki Jihar APC Karo Na 3 a Jere

Jami'an tsaro sun tare hanyar da ta nufi majalisar

Majiyar ta ce jami’an tsaro sun tare hanyar Shendam saboda kada masu zanga-zangar su samu damar wuce wa harabar majalisar, amma suna barin masu ababan hawa don ci gaba da harkokinsu na yau da kullum.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Masu zanga-zangar sun tabbatar da cewa suna bukatar Daniel Ogazi ne kawai a matsayin kakakin majalisar inda suka ce sun gaji da daura wadanda mutane ba sa son su a matsayin shugabannin majalisar.

Masu neman takarar kujerar majalisar

Tsohon kakakin, Balarabe Abdullahi da Daniel Ogazi da Danladi Jatau dukkansu sun nuna sha’awarsu ta tsaya wa takarar shugabancin majalisar ta bakwai.

Dukkansu ‘yan jam’iyyar APC ne wadanda za su gwabza don neman kujerar tare da neman kuri’un ‘yan jam’iyyarsu da ma ‘yan jam’iyyun adawa a majalisar.

Kara karanta wannan

Karon Farko: Majalisar Dattawa Ta Yiwa Tinubu Gata, Ta Amince Ya Yi Wasu Manyan Nade-Nade 20

A ranar Talata 6 ga watan Yuni, magatakardan majalisar, Ibrahim Musa a wata sanarwa ya ce an daga kaddamar da majalisar ta bakwai har sai baba ta gani saboda barazanar tsaro.

Wasu Daga Cikinku Sun Mun Zagon Kasa a Lokacin Zabe, Cewar Gwamna Sule

A wani labarin, gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya bayyana wasu daga cikin mukarrabansa na masa zagon kasa.

Sule ya bayyana haka ne a wani taron bankwana da mambobin majalisar jihar wanda ya gudana a birnin lafia.

Asali: Legit.ng

Online view pixel