Babban Limamin Masallacin Juma'a Na Fagge a Kano Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Babban Limamin Masallacin Juma'a Na Fagge a Kano Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Allah ya yiwa tsohon Wazirin Kano kuma babban limamin masallacin Juma'a na Fagge rasuwa a ranar Laraba, 7 ga watan Yuni
  • Sheikh Nasir Muhammad Nasir wanda aka fi sani da limamin Waje ya rasu ne yana da shekara 87 a duniya bayan ya yi rashin lafiya
  • Babban limamin an taɓa naɗa shi sarautar Wazirin Kano, kafin tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya cire shi

Jihar Kano - Babban limamin masallacin Juma'a na Fagge, Sheikh Nasir Muhammad Nasir, ya riga mu gidan gaskiya, rahoton jaridar Punch ya tabbatar.

Babban malamin ya rasu ne a ranar Laraba 7 ga watan Yuni bayan ya yi fama da jinyar rashin lafiya, za a gudanar da jana'izarsa ranar Alhamis (yau) 8 ga watan Yuni a fadar sarkin Kano.

Babban limamin masallacin Juma'a a Kano ya rasu
Sheikh Nasir Muhammad Nasir ya rasu yana da shekara 87 Hoto: Dateline.com
Asali: UGC

Malamin addinin musuluncin wanda aka fi sani da Limamin Waje ya rasu yana da shekara 87 a duniya.

Kara karanta wannan

'Dan APC Ya Nemi EFCC Ta Cafke Emefiele da Wasu Ministocin Buhari Nan da Kwana 14

Marigayi sarkin Kano Ado Bayero, ya taɓa naɗa marigayin sarautar Wazirin Kano, amma tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya cire shi daga sarautar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kwankwaso ya maye gurbinsa ne saboda dalilan tsaro amma marigayin ya ƙi yarda ya sauka daga kan sarautar.

An yi masa sarautar Wazirin Kano

Marigayi Ado Bayero, ya naɗa Sheikh Nasir matsayin Wazirin Kano ne bayan rasuwar mai riƙe da sarautar a ranar 2 ga watan Agustan 2013.

Gwamnatin jihar a wancan lokacin ta Rabiu Kwankwaso ta ƙi amincewa da naɗin Sheikh Nasir a matsayin Wazirin Kano, amma marigayi Ado Bayero ya haƙiƙance inda ya naɗa masa rawani a wani ɗan ƙaramin biki a fadar sarkin Kano.

Daga baya gwamnatin Kwankwaso ta cire shi daga sarautar. Amma duk da haka marigayin ya ci gaba da ɗaukar kansa a matsayin Wazirin Kano duk da an ba wani daban sarautar, cewar rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

Tsohon Ɗan Takarar Gwamna Ya Kara Jiƙa Wa PDP Aiki Kwanaki Kaɗan Bayan Rantsar da Tinubu

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya aike da saƙon ta'aziyyarsa ga iyalan mamacin, ɗalibansa da al'ummar jihar Kano.

Rijistaran BUK Ya Rasu

A wani labarin na daban kuma, Allah ya yiwa rijistaran jami'ar Bayero da ke jihar Kano (BUK) rasuwa.

Malam Ahmad Jamil Salim ya yi bankwana da duniya a ranar 26 ga watan Afirilun 2023 yana da shekara 60.

Asali: Legit.ng

Online view pixel