Asiri Ya Tonu: ’Yan Sanda Sun Yi Nasarar Kwamushe Rikakken Barawon Shanun da Ya Adabi Jama'a

Asiri Ya Tonu: ’Yan Sanda Sun Yi Nasarar Kwamushe Rikakken Barawon Shanun da Ya Adabi Jama'a

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ta tabbatar da kama wani matashi da ake zargi da satar shanu da kudinsu ya kai N7m
  • Sale Kabo, wanda ake zargin ya fito ne daga kauyen Bandila da ke karamar hukumar Gulani cikin jihar Yobe
  • Kakakin rundunar a jihar, Mahid Abubakar shi ya bayyana haka inda ya ce Sale Kabo ya amsa laifukan da ake tuhumarsa akai

Jihar Gombe – Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ta kama wani matashi da ake zargi da satar shanu har na N7m a jihar.

Wanda ake zargin mai suna Sale Kabo dan shekara 30 ya fito ne daga kauyen Bandila a karamar hukumar Gulani ta jihar Yobe.

'Yan sanda sun kama barawon shanu a Gombe
Sale Kabo, Barawon Shanun da Aka Kama. Hoto: Tribune.
Asali: Facebook

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Gombe, ASP Mahid Abubakar ne ya bayyana haka inda yace Kabo ya sace shanun ne a karamar hukumar Funakaye da ke cikin jihar Gombe, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Rashin Daraja: DJ Ya Addabi 'Yan Islamiyya da Kida Ya Gamu da Fushin Alkali

Wani dattijo a kauyen ne ya kawo rahoton ga rundunar 'yan sanda

Ya bayyana cewa Jauro Ahmadu mai shekaru 75 na kauyen Shuwari a cikin Bajoga da ke karamar hukumar Funakaye ne ya kawo rahoton hedkwatar ‘yan sanda na yanki da ke Bajoga.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mahid ya ce Ahmadu ya tabbatar da cewa an sace masa shanu 21 da kudinsu ya kai N7m a kauyen da tsakiyar dare, cewar Punch.

Tuni rundunar 'yan sandan ta umarci da a fara bincike kan satar shanun

Kakakin ya kara da cewa, rundunar ta umarci da a fara gabatar da bincike don sanin tushen lamarin da kuma dakile sace-sacen shanu a jihar gaba daya nan gaba.

A cewarsa:

“Bayan bincike mai zurfi, an yi nasarar kama Sale Kabo dumu-dumu a satar shanun wanda ya tabbatar da cewa shi ya sace su, yayin da dukkan shanun da ake zargin an sace aka same su a hannunsa da sauran abubuwan da ke da alaka da satar.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Gana da Shugabannin Tsaro Bayan Yan Bindiga Sun Kashe Rayuka 37, Ya Ɗauki Matakai Masu Kyau

“Wanda ake zargin yanzu haka ya na hannun jami’an ‘yan sanda kuma za a tasa keyarsa zuwa kotu da zarar bincike ya kammala."

Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Yarinya Mai Shekaru 7 Bayan Artabu da Jami’an Tsaro a Abuja

A wani labarin, 'Yan bindiga sun yi awun gaba da wata yarinya 'yar shekara 7 a kauyen Yangoji a Kwali da ke Abuja.

Maharan sun kai harin ne a safiyar Laraba 7 ga watan Yuni a Kauyen inda suka yi gumurzu kafin sace yaran.

Asali: Legit.ng

Online view pixel