Gwamna Aliyu Ya Tallafawa Mutanen da Harin Yan Bindiga Ya Shafa a Sakkwato

Gwamna Aliyu Ya Tallafawa Mutanen da Harin Yan Bindiga Ya Shafa a Sakkwato

  • Gwamnan Sakkwato tare da tawagarsa sun ziyarci garuruwan da 'yan bindiga suka kai harin rashin imani ranar Asabar
  • Ahamad Aliyu ya tallafawa iyalan da harin ya shafa da kuɗaɗe da kuma kayan abinci domin rage musu kuncin rayuwa
  • Ya kuma roki mazauna kauyukan su bai wa jami'an tsaron da aka girke a yankin haɗin kai kuma su tona asirin duk wani imfoma

Sokoto - Gwamna Ahmad Aliyu na jihar Sakkwato ya tallafawa iyalan waɗanda suka mutu a harin ranar Asabar domin rage radaɗi da ƙuncin rayuwar da suka shiga.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa gwamna Aliyu ya baiwa iyalan tallafin kuɗi da kuma kayan abinci. Haka nan waɗanda suka ji raunuka da asarar dukiya a harin ya basu tallafin kuɗi.

Gwamna Aliyu.
Gwamna Aliyu Ya Tallafawa Mutanen da Harin Yan Bindiga Ya Shafa a Sakkwato Hoto: Ahmed Aliyu
Asali: Facebook

Idan baku manta ba, wasu 'yan bindiga sun kai hari ƙauyuka uku a yankin ƙaramar hukumar Tangaza, suka kashe mutane 37 yayin da wasu da yawa suka ji raunin harbi.

Kara karanta wannan

Wasu Manyan Jiga-Jigan PDP da Ɗumbin Mambobi Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC a Arewa

Gwamna Aliyu ya ziyarci garuruwan da wannan kazamin hari ya shafa tare da mataimakinsa, Idris Mohammed Gobir, shugabannin hukumomin tsaro da kuma jagoran APC a Sakkwato, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayin wannan ziyara ne tawagar gwamnan suka jajanta da ta'aziyya ga waɗanda harin ya taɓa. An ji gwamnan ya ayyana harin da, "rashin imani da tausayi."

Wane mataki gwamnati ta ɗauka?

Aliyu ya tabbatarwa ɗaukacin al'ummar jihar Sakkwato cewa gwamnatinsa ba zata runtsa ko ta sassauta kan rantsuwar da ta yi na kare rayuka da dukiyoyin mutane ba.

A cewarsa:

"Zamu yi duk mai yuwuwa mu ga wannan kashe-kashen rashin imanin ya zama tarihi a jiharmu."

Bugu da ƙari, ya yi wa mamatan Addu'ar fatan samun sakamko mai kyau a gaban Allah kana ya yi wa waɗanda ke jinya fatan samun sauki cikin ƙanƙanin lokaci.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Gana da Shugabannin Tsaro Bayan Yan Bindiga Sun Kashe Rayuka 37, Ya Ɗauki Matakai Masu Kyau

Ya kuma roƙi mazauna ƙauyukan su taimaka su kai bayanan duk wanda su ke zargin imfoma ne ga hukumomin tsaro kuma su baiwa jami'an tsaron da aka turo haɗin kai.

A cewarsa ta haka ne kaɗai, jami'an zasu cimma nasarar dawo da zaman lafiya a yankunan, kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.

Gwamna Ahmad Aliyu Ya Gana da Shugabannin Tsaro

A wani labarin kuma kun ji cewa Gwamnan Sakkwato ya gana da shugabannin tsaro kan harin da yan bindiga suka kai ranar Asabar.

Sabon gwamnan, wanda ya katse tafiyarsa zuwa Abuja, ya fara ɗaukar matakan kawo karshen 'yan bindiga a jihar da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel