Arewa
Muhammad Badaru, ministan tsaron Najeriya ya yaba da irin yadda Umar Namadi ya ɗauko ayyukan alheri a jihar Jigawa yayin ziyarar da ya kai ta farko ranar Asabar.
Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya amince da biyan naira dubu 35 ga ma'aikatan jihar don rage musu radadi bayan cire tallafin mai a Najeriya baki daya.
Rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta yi nasarar cafke wani matashi mai suna James Isma'il da zargin kisan kai a Sharada da ke karamar hukumar Gwale a jihar.
Akalla yara 10 ne suka samu munanan raunuka bayan wani abin fashewa ya jikkata yaran a kauyen Kidandan da ke karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna.
Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Gwamna Nasir Idris a matsayin gwamnan jihar Kebbi inda ta yi watsi da korafe-korafen dan takarar jam'iyyar PDP.
Gwamnatin jihar Jigawa ta dakatar da daraktan shirin Fadama III da manyan jami'an shirin su 27 saboda zargin karkatar da naira biliyan 1.7 na tallafin COVID-19.
Dan majalisar dokokin jihar Kogi ya tabbatar da rasa rayuka biyu da kadarorin miliyoyin naira a wani rikici da ya ɓalle tsakanin kauyuka 2 a karamar hukumar Ankpa.
Shugaban kasa, Bola Tinubu ya nada Alhaji Aliyu Shehu Shinkafi a matsayin sakataren din-din-din a ma'aikatar albarkatun Ruwa a Abuja don kawo sauyi a bangaren ruwa.
Kotun Shari'ar Musulunci a Bauchi ta ba da umarnin kamo Malam Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi saboda kin mutunta umarnin kotun da ta bukaci ya gurfana a gabanta.
Arewa
Samu kari