Jam’iyyar PDP Ta Girgiza Bayan APC Ta Lamushe Zabukan Ciyamomi 27 da Kansiloli 312 a Borno

Jam’iyyar PDP Ta Girgiza Bayan APC Ta Lamushe Zabukan Ciyamomi 27 da Kansiloli 312 a Borno

  • A jiya Asabar ce 20 ga watan Janairu aka gudanar da zaben kananan hukumomi 27 a jihar Borno da ke Arewacin Najeriya
  • Har ila yau, an gudanar da zaben kansiloli 312 a jihar wanda jam’iyya mai mulki ta APC ta lashe dukkan zabukan
  • Shugaban hukumar zabe a jihar, Lawan Maina shi ya tabbatar da haka a yau Lahadi 21 ga watan Janairu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Borno – Jam’iyyar APC ta lashe zaben dukkan kananan hukumomi 27 da ke jihar Borno a Najeriya.

Har ila yau, jam’iyyar ta kuma lashe dukkan kujerun kansiloli 312 da ke wakiltar unguwanni a jihar.

APC ta lashe zabukan kananan hukumomi 27 da kansiloli 312
Jam'iyyar APC ta lashe zabukan ciyamomi da kansiloli a Borno. Hoto: Babagana Zulum.
Asali: Facebook

Yaushe aka gudanar da zaben?

Kara karanta wannan

Kano: Bayan rashin nasara a Kotun Koli, Ganduje ya sake shirya wargaza shirin NNPP a zabe mai zuwa

An gudanar da zaben ne a jiya Asabar 20 ga watan Janairu inda aka fafata a kananan hukumomin guda 27, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban hukumar zabe a jihar, BOSIEC, Alhaji Lawan Maina shi ya tabbatar da haka a yau Lahadi 21 ga watan Janairu a Maiduguri.

Lawan ya ce biyo bayan gudanar da zaben a jiya Asabar 20 ga watan Janairu sun samu sakamakon zabukan a kananan hukumomi 27.

Mene hukumar zabe ta ce a jihar?

Ya ce:

“Bayan gudanar da zaben a ranar Asabar, a yau mun samu sakamakon zabukan a dukkan kananan hukumomi 27 kamar yadda doka ta tabbatar.
“A matsayina na shugaban hukumar, ina sanar da sakamakon zabukan kamar haka:
“Jam’iyya mai mulki, APC ta lashe dukkan zabukan kananan hukumomi 27 da ke jihar.”

PM News ta tattaro Maina na cewa:

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kama wasu mutane bayan hukuncin Kotun Koli a Kano, an samu karin bayani

“Har ila yau, jam’iyya mai mulkin ta lashe zaben kansiloli 312 a dukkan unguwannin da ke fadin jihar baki daya.
“Dalilin haka, mun kawo karshen wannan zabe, kuma za a ba da satifiket ga wadanda suka samu nasara nan ba da jimawa ba.”

Wannan na zuwa ne yayin da hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta sanar da ranar 3 ga watan Faburairu don gudanar da zaben cike gurbi.

APC ta yi zama kan hukuncin Kotun Koli a Kano

A wani labarin, jam’iyyar APC a jihar Kano ta yi wata ganawa ta musamman bayan hukuncin Kotun Koli a jihar.

Jam’iyyar ta yi zaman ne don duba shari’ar da kuma sake shiri don tunkarar zabukan gaba da za a gudanar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel