Gwamnatin Sokoto Ta Yi Martani Kan Kalaman Batanci Ga Usman Dan Fodiyo, Ta Ba da Shawara Ga Jama'a

Gwamnatin Sokoto Ta Yi Martani Kan Kalaman Batanci Ga Usman Dan Fodiyo, Ta Ba da Shawara Ga Jama'a

  • Gwamnatin jihar Sokoto ta barranta kanta da wasu kalaman batanci da wani ma'aikacin gwamnatin jihar ya yi
  • Gwamnatin ta yi Allah wadai da wadannan kalamai inda ta shawarci mutane kan sanin abin da za su fada
  • Idan ba a mantaba, Babban darakta a hukumar SUBEB, Alhaji Abba Tambuwal ya yi wasu kalamai ga Sheikh Usman Dan Fodiyo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Sokoto - Gwamnatin jihar Sokoto ta yi martani kan munanan kalamai da wani ma'aikacin gwamnatin jihar ya yi kan Shehu Usman Dan Fodiyo.

Gwamna Ahmad Aliyu ya yi Allah wadai da kalaman inda ya ce abin takaici ne a yi hakan ga mutum mai daraja kamar Dan Fodiyo.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da ganawa kan matsalar tikitin Musulmi da Musulmi, Tinubu ya nada dan Arewa babban mukami

Gwamnatin jihar Sokoto ta yi martani kan kalaman batanci gA Sheikh Usman Dan Fodiyo
Gwamna Aliyu ya yi Allah wadai da kalaman da wani ya yi ga Shehu Dan Fodiyo. Hoto: Ahmad Aliyu.
Asali: Twitter

Mene ya jawo cece-kuce a Sokoto?

Idan ba a mantaba, Babban daraktan kudi na hukumar SUBEB dake Sokoto, Alhaji Abba Shehu Tambuwal yayi munanan kalamai kan Sheikh Usman Dan Fodiyo a faifan bidiyo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daraktan yayi wannan furucin ne yayin wani gangamin zabe da suka gudanar na takarar kujerar dan majalisar jiha mai wakiltar Tambuwal ta Yamma wanda za a gudanar a watan Faburairu.

Sakataren yada labaran gwamnan, Abubakar Bawa shi ya bayyana haka a yammacin jiya Litinin 22 ga watan Janairu.

Bawa ya ce gwamnatin jihar ta yi Allah wadai da kalaman kuma ta barranta kanta da kalaman daraktan, cewar Tribune.

Martanin Gwamnan jihar Sokoto

Sanarwar ta ce:

"Gwamnatin jihar Sokoto ta kadu da ganin wani faifan bidiyo da ake yadawa inda wani ya yi kalaman batanci ga Shehu Usman Dan Fodiyo.

Kara karanta wannan

Ibadan: Adadin mutanen da suka mutu yayin da wani abu ya fashe a babban birnin jihar PDP ya ƙaru

"Gwamnatin jihar ta yi Allah wadai da wadannan kalamai tare da barranta kanta da wadannan kalaman batanci.
"Gwamnatin jihar ta yi imani da dukkan koyarwa da kuma akidar Shehu Dan Fodiyo tare da hukumomin da ya jagoranta."

Gwamnatin ta shawarci mutane su guji misali da irin wadannan mutane ma su daraja sai dai idan misali mai kyau ne.

Ta kuma tabbatar da cewa za ta yi bincike kan dalilin kalaman da kuma daukar matakin da ya dace.

Kotun ta ba da sabon umarni kan Dutsen Tanshi

Kun ji cewa kotun shari'ar Musulunci ta ba da umarnin cafke Malam Idris Abdul'aziz.

Wannan na zuwa ne bayan malamin ya ki amsa gayyatar kotun a lokuta da dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel