Gwamnatin Plateau Ta Sanya Dokar Hana Fita Na Tsawon Awanni 24, Bayanai Sun Fito

Gwamnatin Plateau Ta Sanya Dokar Hana Fita Na Tsawon Awanni 24, Bayanai Sun Fito

  • Yayin da rashin tsaro ke kara kamari, gwamnan jihar Plateau ya sanya dokar hana fita a jihar na tsawon awanni 24
  • An kafa dokar ce a karamar hukumar Mangu da ke fama da matsalar tsaro fiye da ko ina a fadin jihar baki daya
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnan jihar, Gyang Bere ya fitar a yau Talata 23 ga watan Janairu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Plateau - Gwamnatin jihar Plateau ta sanya dokar hana fita har na tsawon awanni 24 a jihar.

Dokar za ta shafi karamar hukumar Mangu da ke jihar wacce ta ke fama da hare-haren 'yan bindiga da garkuwa da mutane.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da gobara ta cinye tsohuwa mai shekaru 80 a jihar Benue

Gwamnatin Plateau ta sanya dokar hana fita na tsawon awanni 24
Gwamnatin Plateau Ta Sanya Dokar Hana Fita a Mangu. Hoto: Caleb Mutfwang.
Asali: Facebook

Mene dalilin sanya dokar?

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnan jihar, Gyang Bere ya fitar a yau Talata 23 ga watan Janairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bere ya ce daukar matakin ya zama dole ganin yadda rashin tsaro ke kara tabarbarewa a yankin, cewar Punch.

Sanarwar ta ce:

"Gwamna ya nemi shawarwari daga dukkan masu ruwa da tsaki a harkokin tsaro kafin daukar matakin.
"Ya bayyana cewa iya mutane masu aiki na musamman kadai ne za su iya zirga-zirga a karamar hukumar har sai yadda hali ya yi.
"Ya bukaci 'yan jihar musamman mazauna karamar hukumar Mangu da su bi dokar tare da taimakawa jami'an tsaro don dawo da zaman lafiya."

Gwamnan ya koka kan yadda wasu ke kokarin kawo cikas a zaman lafiya a jihar duk da kokarin da gwamnati ke yi, cewar Channels TV.

Kara karanta wannan

Kano: Tashin hankali yayin da matashi ya sheke abokin aikinsa a Kamfani, matasa sun tafka barna

Martanin gwamnan jihar

Ya kara da cewa:

"Ya koka kan yadda wasu suka kirkiri rashin tsaro a jihar duk da kokarin gwamnatin jihar don ganin ta dakile ayyukan 'yan ta'adda.
"Ya tura sakon jaje ga iyalan wadanda abin ya shafa inda ya yi alkawarin dawo da zaman lafiya a jihar."

Gwamnan har ila yau, ya yi alkawarin sassauta dokar da zarar an samu zaman lafiya ya inganta a yankin, cewar Leadership.

'Yan Majalisu sun sha alwashin komawa kujerunsu

Kun ji cewa 'yan Majalisun jihar Plateau sun sha alwashin komawa kan kujerunsu saboda rashin adalci a hukunci kotu.

'Yan Majalisun 16 sun sha alwashin halartar zaman Majalisar a yau Talata 23 ga watan Janairu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel