Innalillahi: Bam Ya Raunata Yara 10 a Kaduna, Bayanai Sun Fito

Innalillahi: Bam Ya Raunata Yara 10 a Kaduna, Bayanai Sun Fito

  • Jama'ar kauyen Kidandan sun shiga wani yanayi bayan abin fashewa ya jikkata wasu yara guda 10
  • Abin fashewar da ake zargin bam ne ya fashe a kauyen da ke karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna
  • Lamarin ya faru ne da ranar yau Asabar 20 ga watan Janairu inda bam din ya tashi yayin da yaran ke wasa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - An shiga rudani a kauyen Kidandan da ke karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna bayan wani abin fashewa ya raunata yara.

Lamarin ya faru ne da ranar yau Asabar 20 ga watan Janairu inda bam din ya tashi da yara 10 yayin da suke wasa a wurin.

Kara karanta wannan

Satar mutane a Abuja: "Mun kama wasu masu yiwa yan bindiga leken asiri", Wike ya yi karin bayani

Bam ya tashi da wasu yara 10 yayin da suke wasa a Kaduna
Bam Ya Raunata Yara 10 a Kaduna ayin da Suke Je Debo Itace. Hoto: Uba Sani.
Asali: Twitter

Mene dalilin tashin bam din a Kaduna?

An tabbatar da cewa yara 10 dukkansu sun samu raunuka yayin da suke wasa da wani abu da suka samu a cikin daji.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daily Trust ta tattaro cewa abin da yaran ke wasa da shi an tabbatar shi ne ya tarwatse da su.

An bayyana hotunan yaran cikin jini inda mutane suka kawo musu dauki don basu kulawa.

Tuni aka kwashi yaran zuwa asibitin Shika da ke birnin Zaria don samun kulawa ta musamman.

Dagacin kauyen, Alhaji Abubakar Ruka ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce ya na kokarin tattara sunayen yaran.

Martanin mai sarautar gargajiya a yankin

Ya ce:

"Yara 10 sun jikkata, duk da babu mutuwa amma an kwashe su zuwa asibiti, yanzu haka ina tattara sunayensu."

Har ila yau, kansilan da ke wakiltar yankin, Abdullahi Isma'il shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Asabar 20 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Abdullahi Sule: Zanga-Zanga ba za ta sauya nasara ta ba a Kotun Koli

Ya ce lamarin ya rutsa da yaran ne yayin da suka je cikin dajin don dibar itacen girki, cewar Intel Region.

Sai dai kakakin 'yan sanda a jihar, ASP Mansir Hassan bai yi martani ba saboda rashin samun shi a waya.

'Yan bindiga sun hallaka shugaban makaranta

A wani labarin, wasu 'yan bindiga sun hallaka wani shugaban makaranta a jihar Kaduna.

Maharan sun yi ajalin malamin ne bayan ya ki amincewa su tafi da shi inda suka yi garkuwa da matanshi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel