Ana Fargabar Leburori 3 Sun Mutu Sakamakon Kasa da Ya Rufta Musu a Nasarawa

Ana Fargabar Leburori 3 Sun Mutu Sakamakon Kasa da Ya Rufta Musu a Nasarawa

  • Akalla mutane uku ne ake fargabar sun mutu bayan da kasa ta zabtare ta fada kansu a lokacin da suke hakar jar kasa a jihar Nasarawa
  • Rahotanni sun bayyana cewa leburori hudu ne ke aikin hakar kasar a lokacin da ta zabtare, amma daya daga cikin su ya samu damar kubuta
  • Tun a ranar Lahadi lamarin ya faru, sai dai har zuwa yanzu ba a iya gano inda gawarwakin mutanen uku suke ba, amma ana kan nema

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Nasarawa - Ana fargabar wasu leburori uku sun mutu bayan da wata zaftarewar kasa ta afku a Unguwan Ayaba da ke karamar hukumar Keffi a jihar Nasarawa, a yammacin ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da yan bindiga suka sace matafiya a titin Ondo-Ekiti

Ma’aikatan suna ta tono jar kasa tare da lodawa a cikin wata mota a kauyen, sai kwatsam kasar ta zabtare ta fado tare da binne hudu daga cikinsu.

Leburori uku sun mutu a Nasarawa
Ana fargabar leburori 3 sun mutu sakamakon kasa da ya rufta musu a Nasarawa. Hoto: @LeadershipNGA
Asali: Twitter

An ce daya daga cikinsu ya yi sa’a domin ya samu nasarar kubuta amma ya samu raunuka yayin da sauran ukun suka gamu da ajalinsu, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har yanzu ana kan kokarin ciro gawar leburorin

Masu aikin ceto da mutanen kauyen sun isa wurin domin dauko gawarwakin leburori uku, tun ranar Lahadi amma har zuwa yanzu abin ya ci tura.

Daya daga cikin masu aikin ceton, Saliu Abdullahi, bayan shafe awanni biyu suna hakar kasar, ya ce ba za su bar wurin ba har sai sun ciro gawarwakin ma’aikatan uku.

Shima mataimakin shugaban kungiyar masu motar 'tifa' dake karamar hukumar Keffi, Aminu Sunusi, ya ce sun aika da injin tonar kasa domin a gaggauta aikin ceton.

Asali: Legit.ng

Online view pixel