Arewa
Tsohon kwamishinan ayyuka na musamman a gwamnatin Yahaya Bello na jihar Kogi, Kwamared Yahaya Isma'il, ya rasu ranar Litinin da yamma, an masa jana'iza.
Kotun Koli ta tanadi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan jihar Nasarawa da ke kalubalantar zaben Gwamna Sule Abdullahi a jihar wanda ya yi nasara a jam'iyyar APC.
Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya yi godiya ga 'yan jihar bayan ya samu nasara a shari'ar zabe a Kotun Koli a ranar Juma'a 12 ga watan Janairu a Abuja.
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa (NSEMA) reshe jihar Neja ta bayyana cewa na samu rahoton hatsarin jirgin ruwa a jihar wanda ya rutsa da mutane akalla 100.
Rundunar 'yan sanda a jihar Kaduna ta tabbatar da cafke wani matashi da ake zargin ya sace janareton masallacin Juma'a mai amfani da hasken rana a jihar.
Karamin Ministan Tsaro a Najeriya, Bello Matawalle ya amince don yin aiki tare da Gwamna Dauda Lawal Dare na jihar Zamfara musamman bangaren rashin tsaro.
Tsohon gwamnan jihar Plateau, Jonah Jang ya soki hukuncin Kotun Daukaka Kara da ta rusa zaben 'yan Majalisun Tarayya da jihohi a jihar da cewa babu adalci.
Mayakan ISWAP sun yanke danyen hukunci kan wasu masunta guda biyu bayan da suka kama su kan zargin sun yi masu satar kifi a wani kauyen jihar Borno.
Kotun Koli ta raba gardama a shari'ar zaben gwamnan jihar Plateau inda ta tabbatar da cewa Gwamna Caleb Mutfwang na jihar shi ya yi nasara a shari'ar.
Arewa
Samu kari