Kotun Koli Ta Sake Yanke Hukuncin Karshe Kan Shari'ar Neman Kifar da Gwamnan Kebbi

Kotun Koli Ta Sake Yanke Hukuncin Karshe Kan Shari'ar Neman Kifar da Gwamnan Kebbi

  • Kotun Koli ta yanke hukuncin karshe kan takaddamar zaben gwamnan jihar Kebbi a Arewacin Najeriya
  • Kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Nasir Idris na jam'iyyar APC a matsayin halastaccen gwamnan jihar
  • Kotun kuma har ila yau, ta yi fatali da korafe-korafen dan takarar jam'iyyar PDP, Aminu Bande saboda rashin hujjoji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kotun Koli ta yi hukunci kan takaddamar shari'ar zaben gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris.

Kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Nasir Idris na jam'iyyar APC a matsayin halastaccen gwamnan jihar, cewar Channels TV.

Kotun Koli ta yi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan Kebbi
Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Gwamna Nasir Idris a matsayin gwamna. Hoto: Nasir Idris.
Asali: Facebook

Wane hukunci kotun ta yanke kan shari'ar Kebbi?

Har ila yau, kotun ta yi fatali da korafe-korafen dan takarar jam'iyyar PDP, Aminu Bande saboda rashin gamsassun hujjoji.

Kara karanta wannan

Kotun Koli ta yi hukuncin karshe a shari'ar neman tumbuke gwamnan Gombe, ta fadi dalillai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin hukuncin, dukkan alkalan kotun sun amince da cewa korafe-korafen dan takarar PDP ba su da tasiri kamar yadda Kotun Daukaka Kara ta yi hukunci.

A baya, Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da nasarar Gwamna Nasir Idris na APC a matsayin zababben gwamnan jihar.

Yayin da kuma ta yi watsi da karar Bande wanda ya yi takara a jam'iyyar PDP a zaben na watan Maris, cewar The Nation.

Sauran hukunce-hukuncen da Kotun Koli

Tun farko, Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta tabbatar da nasarar Gwamna Nasir Idris a matsayin wanda ya lashe zaben.

Aminu Bande a bangarensa, ya kalubalanci zaben da aka gudanar a watan Maris da cewa akwai kura-kurai cike a ciki.

Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da sauraran shari'ar zabukan jihohi da dama a Kotun Koli da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Kotun Koli ta yanke hukuncin karshe kan shari'ar neman tsige gwamnan APC, akwai dalilai

Kotun Koli ta yi hukunci a zaben jihar Gombe

Kun ji cewa Kotun Koli ta yi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan jihar Gombe a yau Juma'a.

Kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Inuwa Yahaya na jami'yyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar.

Yayin da ta yi watsi da korafe-korafen dan takarar jam'iyyar PDP a zaben, Jibrin Barde saboda rashin gamsassun hujjoji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel