Kano: Tashin Hankali Yayin da Matashi Ya Sheke Abokin Aikinsa a Kamfani, Matasa Sun Tafka Barna

Kano: Tashin Hankali Yayin da Matashi Ya Sheke Abokin Aikinsa a Kamfani, Matasa Sun Tafka Barna

  • 'Yan sanda a jihar Kano sun yi nasarar cafke wani matashi da zargin kisan kai a cikin wani kamfani
  • Wanda ake zargin mai suna James Isma'il ya yi ajalin abokin aikinsa mai suna Tukur Adamu a kamfanin
  • Lamarin ya faru ne a kamfanin Fas Agro da ke Sharada a karamar hukumar Gwale da ke jihar Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta tabbatar da cafke wani matashi da zargin kisan kai a jihar.

Ana zargin James Isma'il da kisan kai a kamfanin Fas Agro da ke Sharada a karamar hukumar Gwale da ke jihar.

Kara karanta wannan

Kano: Yayin da rashin tsaro ya addabi Arewa maso Yamma, yan sanda sun dauki muhimmin mataki a jihar

Yan sanda sun cafke matashi kan zargin kisan kai a Kano
Matashin ya shiga hannun 'yan sanda kan zargin kisan kai. Hoto: NPF.
Asali: Twitter

Mene ake zargin matashin a Kano?

Kwamishinan 'yan sanda a jihar, Hussaini Gumel shi ya tabbatar da haka ga manema labarai a yau Lahadi 21 ga watan Janairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gumel ya ce an yi kisan ne a kamfanin da ke Sharada yayin da suka samu rahoton kisan da misalin karfe 8:30 na safe.

Ya ce da isar jami'ansu kamfanin, sun tabbatar da cewa fada ce ta kaure tsakanin James Isma'il da kuma wani mai suna Tukur Adamu duk masu shekaru 32.

Ya kara da cewa a lokacin fadan, Tukur ya fadi kasa inda aka dauke shi zuwa asibiti yayin da likita ya tabbatar da mutuwar shi, cewar Daily Post.

Yawan matasan da aka kama a Kano

Ya ce:

"Lamarin ya tayar da hankalin wadanda ke cikin kamfanin da kuma jama'ar yankin baki daya.

Kara karanta wannan

Kamar Tinubu, Gwamnan Arewa ya amince da biyan ma'aikata N35,000 don rage radadin cire tallafi

"Jami'anmu sun yi kokari wurin gano wanda ake zargi da aikata kisan, James Isma'il inda tuni aka kama shi.
"Saboda abin da ya faru matasa sun yi amfani da wannan dama inda suka fara satar kaya da kuma kokarin cinna masa wuta."

Gumel ya ce yanzu haka an kama matasa fiye da 15 da ake zargin da hannunsu a faruwar lamarin.

Da ake tuhumarshi, James ya ce wannan abin da ya faru tsautsayi ne inda ya ce ko kai masa hannu bai yi ba.

Ya ce tun farko marigayin ne ya fara zagin iyayensa inda shi ma ya rama, daga nan suka cakwame juna yayin da Tukur ya fadi kasa shikenan.

'Yan sanda a Kano sun tsaurara tsaro

A wani labarin, rundunar 'yan sanda a Kano ta tsaurara tsaro a iyakokin jihar don inganta tsaro a fadin jihar.

Wannan na zuwa ne yayin da Arewa maso Yamma ke fama da matsanancin rashin tsaro da hare-haren 'yan bindiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel