Kotun Shari'ar Musulunci Ta Dauki Sabon Mataki Kan Shari'ar Idris Dutsen Tanshi, Ta Fadi Dalilai

Kotun Shari'ar Musulunci Ta Dauki Sabon Mataki Kan Shari'ar Idris Dutsen Tanshi, Ta Fadi Dalilai

  • Yayin da ake ci gaba da shari'ar Malam Idris Abdul'aziz, Kotun Shari'ar Muslunci ta sake daukar sabon mataki
  • Kotun ta umarci sake kama Malam Idris saboda rashin mutunta umarnin kotun na halartar shari'ar
  • Bayanai sauraran korafe-korafen dukkan bangarorin biyu, alkalin kotun ya ce dole wanda ake zargin ya gurfana a gaban kotun

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Bauchi - Kotun Shari'ar Musulunci da ke jihar Bauchi ta sake umartar kama Dakta Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi.

Kotun ta dauki matakin ne kan kin halartar zaman kotun don ci gaba da shari'ar da ake yi, cewar Tribune.

Kotun Shari'ar Musulunci ta yi hukunci kan Idris Abdul'aziz
Kotun Shari'ar Musulunci ta umarci cafke Idris Dutsen Tanshi. Hoto: Sheikh Idris Abdul'aziz.
Asali: Facebook

Wane mataki kotun ta dauka kan Sheikh Idris?

Kara karanta wannan

Kotun Koli ta jingine hukunci kan shari'ar zaben neman tsige gwamnan Kaduna, komai na iya faruwa

Mai Shari'a, Malam Hussaini A. Turaki ya ki amincewa da korafin lauyan wanda ake kara kan umarnin Kotun Daukaka Kara a Jos.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayanai sauraran korafe-korafen dukkan bangarorin, alkalin kotun ya ce dole wanda ake zargin ya gurfana a gaban kotun duk belin da aka bayar a baya.

Lauyan masu karar, UB Umar da ke ma'aikatar Shari'a a jihar ya ce sun tura masa sako don ya halarci zaman kotun amma ya bayyana a fili cewa ba zai zo ba.

Ana dai tuhumar Dakta Idris ne da laifuka biyu, na farko kalaman batanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. da kuma laifin tayar da zaune tsaye.

Martanin lauyoyin ko wane bangare

Ya ce:

"Mun tura masa takardar halartar kotu amma ya ki amsa gayyatar inda a bayyane ya ce ba zai zo ba.
"Kotun ta umarce shi da ya zo kotun ya tabbatar mata me yasa ba zai zo ba a zaman da ya gabata, idan ya ba da hujjoji shikenan.

Kara karanta wannan

Matashi ya gurfana a kotu kan zargin taba muhibbar malamin addini a Kano

"Mun tura gayyata ya ki ya zo, mun bi duk wata hanya bai zo ba, abu na gaba shi ne shaidar kamu daga jami'an tsaro wanda za mu kawo shi zuwa ranar 24 ga watan Janairu."

A bangarenshi, lauyan wanda ake zargin, Ahmad M Umar ya ce duk da umarnin cafke malam, ya kamata kotun ta mutunta umarnin Kotun Daukaka Kara a Jos.

Kotun ta dage ci gaba da sauraran shari'ar har ranar 24 ga watan Janairun wannan shekara, cewar Leadership.

An kama mahaifi zai siyar da ɗan cikinsa

A wani labarin, Hukumar NSCDC ta cafke wani mahaifi yayin da ya ke kokarin siyar da ɗan cikinsa a Abuja.

Mahaifin yaron ya ce halin yau ne ya saka shi yanke wannan shawara na siyar da ɗan nasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel