Mutane Sun Mutu Yayin da Wani Sabon Rikici Ya Ɓarke a Jihar Arewa, An Takfa Babbar Asara

Mutane Sun Mutu Yayin da Wani Sabon Rikici Ya Ɓarke a Jihar Arewa, An Takfa Babbar Asara

  • An rasa rayuka da dukiya mai dimbin yawa yayin rikicin kalibalanci ya ɓarke tsakanin mazauna kauyuka biyu a jihar Kogi
  • Mamba mai wakiltar mazaɓar Ankpa 1, Honorabul Lawal ya tabbatar da lamarin tare da kira ga mahukunta su kai agajin gaggawa
  • Rundunar yan sanda ta bayyana cewa CP ya ziyarci garuruwan da rikicin ya shafa kuma zaman lafiya ya dawo kamar baya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kogi - An kashe mutane biyu, yayin da aka kona gidaje sama da 70 a rikicin kabilanci da ya barke tsakanin wasu ƙauyuka biyu a jihar Kogi.

Ƙauyukan da rikicin kabilanci ya rutsa da su sun hada da Oturpo-Ojile da Ochi-Ibadan da ke karkashin karamar hukumar Ankpa da ke jihar, Channels tv ta tattaro.

Kara karanta wannan

Gyadar dogo: Mutanen da suka sha da kyar da aka kifar da Gwamnatin Najeriya a 1966

Rikicin kabilanci ya jawo asara a Kogi.
Mutim 2 sun mutu, gidaje 70 sun ƙone a wani sabon rikicin kaiyuka a jihar Kogi Hoto: PoliceNG
Asali: Twitter

Rikicin ya samo asali ne lokacin da wasu mazauna garin Ochi-Ibadan suka kashe wani mutum dan ƙauyen Oturpo-Ojile a hanyarsa ta dawowa daga Legas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakamakon haka cikin fushin kisan ɗan uwansu, wasu matasan kauyen Oturpo-Ojile suka kai harin ɗaukar fansa, inda suka ƙona gidaje tare da lalata dukiyar miliyoyi a Ochi-Ibadan.

Ɗan majalisa ya faɗi illar da rikicin ya haifar

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Ankpa I, Akus Lawal, shi ne ya tabbatar da faruwar lamarin a zauren majalisar dokokin jihar Kogi yayin zamansu na ranar Alhamis.

Ya ce lamarin ya faru ne a ranar 14 ga watan Junairu, 2024, inda ya ce rikicin kabilanci da aka yi tsakanin kauyukan biyu ya tayar da hankali matika don haka bai kamata a bar irin haka ta sake afkuwa ba.

Ya kuma yi kira ga hukumar ba da agajin haggawa ta jihar Kogi da ta hanzarta kai kayan agaji ga duk wadanda rikicin kabilancin ya shafa a garuruwan 2.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Ƴan bindigan da suka sace shugaban ƙaramar hukuma sun turo saƙo mai ɗaga hankali

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka

Da yake tabbatar da faruwar lamarin ta wayar tarho, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP William Aya, ya ce an tura tawagar ‘yan sanda zuwa wurin.

Ya ce fusatattun matasan sun kashe wani mai suna, Samuel Peter da karin mutum guda da ba a gano bayanansa ba, rahoton Leadership.

Kakakin ƴan sandan ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Bethrand Onuoha, ya ziyarci garuruwan biyu kuma tuni aka dawo da zaman lafiya.

An samu ƙarin waɗanda suka mutu a Ibadan

A wani rahoton kuma Gwamnatin Oyo karkashin Gwamna Makinde ta yi ƙarin haske kan yawan mutanen da suka mutu a fashewar da ta afku a Ibadan.

Mai ba gwamna shawara na musamman kan tsaro, Fatai Owoseni, ya ce adadin mamatan ya ƙaru zuwa 5 a yau Alhamis da safe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel