Abun Bakin Ciki
Mace ta farko da ta zama Manjo Janar a Najeriya, Aderonke Kale mai ritaya ta riga mu gidan gaskiya ta na shekaru 84 a duniya a birnin Landan da ke Ingila.
Kasa da awanni 24 da su ka rage a gudanar da zaben jihar Kogi, shugaban karamar hukumar Lokoja a jihar, Muhammad Danasabe ya riga mu gidan gaskiya.
Yayin da rikici ya ki ci ya ki cinyewa, Isra'ila ta dauki matakin tsagaita wuta na awanni hudu a ko wace rana don bai wa fararen hula damar ficewa a Arewacin Gaza.
Wani mutum-mutumi ya kasa wani mutum a kamfanin sarrafa barkono a Koriya ta kudu, bayan ya dauke shi a matsayin kwalin kayan lambu. An saba samun irin haka a kasar.
Yayin da ake ci gaba da shari'ar kisan gillar Janar Alkali, lauya mai gabatar da kara, Simon Mom ya gabatar shaida a rubuce na Timothy da ake zargi a kisan.
An samu asarar rai yayin da wasu mutane biyar su ka jikkata yayin rikicin zaben shugabancin ma su gidajen haya a Anambra, an lalata gidaje da ababan hawa.
Mai maganin bindiga ya yi ajalin wani mutum yayin gwada maganin bindiga a cikin daji, 'yan sanda sun cafke mutane biyu kan zargin hadin baki da kisan kai.
Rundunar 'yan sanda ta cafke wasu 'yan fashi guda hudu kan zargin hallaka dan uwansu saboda ya mu su baba-kere da kayan ganima da su ka sa mu yayin gudanar da sata.
Hukumar NSCDC ta cafke wata mata mai suna Folasade kan zargin damfarar gidan marayu da ta ke aiki har naira miliyan daya, an gano wasu abubuwa a wurinta.
Abun Bakin Ciki
Samu kari