Ana Neman Ganin Karshen Netanyahu, Ya Gaza Kafa Gwamnati a Zaben Isra'ila

Ana Neman Ganin Karshen Netanyahu, Ya Gaza Kafa Gwamnati a Zaben Isra'ila

  • Sakamakon ƙarshe na zaɓen Isra’ila ya nuna cewa kawancen jam’iyyun Firaminista Benjamin Netanyahu ya samu kujeru 53 cikin 120 na majalisar dokokin ƙasar
  • Kawancen hamayya ya samu kujeru 48, yayin da ƙungiyoyin jam’iyyun Larabawa suka samu kujeru 19, lamarin da ya sanya su zama masu tasiri wajen kafa sabuwar gwamnati
  • Zargin yiwuwar katsalandan daga ƙasashen waje ya ƙara dagula al’amuran siyasar ƙasar, yayin da hukumomin tsaro da na zaɓe ke binciken zarge-zargen da aka yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Isra’ila – Sakamakon ƙarshe na babban zaɓen Isra’ila ya nuna cewa kawancen jam’iyyun Firaminista Benjamin Netanyahu ne ya samu mafi yawan kujeru, amma bai kai adadin da ake buƙata domin kafa gwamnati shi kaɗai ba.

Kawancen Netanyahu, wanda ya ƙunshi jam’iyyun masu tsattsauran ra’ayin, ya samu kujeru 53 cikin 120 na majalisar dokokin Isra’ila, wadda aka fi sani da Knesset.

Kara karanta wannan

An yi taru don hada kan 'yan adawa a kifar da Tinubu a gidan babban fasto

Benjamin Netanyahu
Benjamin Netanyahu a Isra'ila. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

France24 ta wallafa cewa har yanzu kawancen yana da ƙarancin kujeru takwas kafin ya kai mafi ƙarancin kujeru 61 da ake buƙata domin samun rinjaye a majalisar.

Netanyahu ya samu kujeru 53

Sakamakon da Hukumar Zaɓe ta Isra’ila ta fitar a ranar Juma’a ya nuna cewa jam’iyyar Likud ta Netanyahu ce ta fi kowace jam’iyya samun kujeru, inda ta samu 27.

Rahoto ya kuma nuna cewa kawancen jam’iyyun hamayya, wanda Gadi Eisenkot ke jagoranta, ya samu kujeru 48.

Wannan sakamako ya nuna cewa babu wani kawance da ya samu rinjayen kujeru 61 da ake buƙata domin kafa gwamnati ba tare da neman goyon bayan wasu jam’iyyun ba.

Saboda haka, ana sa ran za a shafe makonni ana tattaunawa domin samar da kawancen da zai iya kafa gwamnati mai ɗorewa. Idan tattaunawar ta gaza, yiwuwar sake gudanar da zaɓe na nan.

Jam’iyyun Larabawa taka rawa

Ƙungiyoyin jam’iyyun Larabawa biyu, Raam da Joint List, sun samu kujeru 19 a tsakaninsu, lamarin da ya sanya su cikin waɗanda za su iya taka muhimmiyar rawa wajen kafa sabuwar gwamnati.

Kara karanta wannan

Netanyahu ya samu matsala a zaben Israila, an ji halin da kujerarsa ke ciki

BBC ta wallafa cewa rashin samun rinjaye da kowanne bangare ya yi na iya sa kawancen Netanyahu da na hamayya su nemi goyon bayan wasu jam’iyyun domin samun kujerun da za su kai su ga rinjaye.

Sai dai har yanzu ba a tabbatar da yadda tattaunawar kawancen za ta kasance ba, ko kuma wane bangare ne zai samu damar kafa gwamnati.

Wajen zaben Isra'ila
Yadda wani mutum ke kada kuri'a a zaben Isra'ila. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Netanyahu ya yi korafi

A wani labarin, kun ji cewa shugaban hukumar da ke kula da zaɓukan Isra’ila ya nemi a gudanar da bincike kan yiwuwar katsalandan daga wasu ƙungiyoyin ƙasashen waje.

Matakin ya biyo bayan zarge-zargen Netanyahu da wasu abokan siyasarsa na cewa yawan fitowar Larabawa ’yan ƙasar Isra’ila domin kaɗa ƙuri’a na iya shafar sakamakon zaɓen.

Shugaban hukumar zabe ya rubuta wa Shin Bet wasiƙa, inda ya buƙaci hukumar tsaron ta binciki zargin kuɗin da ake cewa wasu masu ruwa da tsaki daga ƙetare sun bayar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng