Kwana 2 da Bude Iyakoki, Kwastam Ta Samu Gagarumar Nasara, Bayanai Sun Fito

Kwana 2 da Bude Iyakoki, Kwastam Ta Samu Gagarumar Nasara, Bayanai Sun Fito

  • Yayin da ake cikin watan azumi mai alfarma, an cafke kwantena dauke da muggan makamai a jihar Legas
  • Hukumar Kwastam a tsibirin Tin-Can a jihar ita ta tabbatar da haka a yau Juma'a 15 ga watan Maris
  • Daga cikin kayan da aka cafke ban da makaman akwai miyagun kwayoyi da kuma kayan sojoji a yayin bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Legas - Hukumar Kwastam a yankin tsibirin Tin-Can ta cafke kwantena dauke da mugayen makamai ana kokarin shigo da su Najeriya.

Bayan muggan makaman, daga cikin kayan da hukumar ta cafke akwai kayan sojoji da miyagun kwayoyi.

Hukumar Kwastam ta yi nasarar dakile shigo da muggan makamai Najeriya
Hukumar Kwastam ta cafke makamai da miyagun kwayoyi a Legas. Hoto: Nigerian Customs Service.
Asali: Getty Images

Yadda Kwastam ta yi nasarar cafke makamai

Kara karanta wannan

Gwamna Uba Sani ya tona asirin inda aka kai daliban da aka sace a Kaduna, bayanai sun fito

Daily Trust ta tabbatar da cewa an yi nasarar kama kayan ne bayan binciken kwantena da ke kokarin shiga da su Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har zuwa lokacin tattara wannan rahoto ba a samu labarin ko an cafke wasu dalilin haka ba.

A cikin kayan da hukumar ta yi nasarar cafkewa akwai bindigu da dama masu sarrafa kansu da kuma kananan makamai, cewar Channels TV.

Wannan na zuwa ne yayin da Najeriya ke fama da matsalar tsaro wanda ake ganin na da alaƙa da iyakokin kasar.

Kwastam ta yi magana kan bude iyakoki a Najeriya

Har ila yau, Kwanturolan hukumar Kwastam, Adewale Adeniyi ya ce Shugaba Tinubu ne kadai ke da damar bude iyakar Najeriya.

Adeniyi ya bayyana haka ne a ranar Asabar 9 ga watan Maris a garin Kongolam, a karamar hukumar Mai’adua da ke jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Yayin da ake cikin wani hali, Tinubu ya bada umarnin bude iyakokin Najeriya, bayani sun fito

Kwanturolan ya kuma ziyarci tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari inda ya ba shi tabbacin samar da sauki ga ‘yan kasuwa a kan hanyoyi.

Tinubu ya bude iyakar Najeriya

Kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin bude iyakokin da ke tsakanin Najeriya da kasar Nijar.

Matakin ya shafi iyakokin sama da kuma na tudu da sauran dokoki da aka kakabawa kasar Nijar a kwanakin baya.

Tinubu ya dauki wannan mataki ne yayin da ake ta kiraye-kirayen a bude iyakokin Najeriya domin samun sauƙin rayuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel