Ana Alhinin Mutuwar Dalibai a Nasarawa, Mata 4 Sun Mutu Yayin Karbar Zakka a Bauchi

Ana Alhinin Mutuwar Dalibai a Nasarawa, Mata 4 Sun Mutu Yayin Karbar Zakka a Bauchi

  • Ana jimamin mutuwar dalibai a jihar Nasarawa, wasu mata sun sake rasa rayukansu yayin cunkoson karbar Zakka a Bauchi
  • Matan sun rasu ne a yau Lahadi 24 ga watan Maris yayin cunkoson karbar Zakka da mai kamfanin mai na AYM Shafa ke bayarwa
  • Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, SP Ahmed Wakili ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Lahadi 24 ga watan Maris

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Bauchi - Akalla mata huɗu ne suka rasa rasa rayukansu yayin karbar Zakka a jihar Bauchi da ke Arewacin Najeriya.

Tribune ta tabbatar da cewa matan sun tsinci kansu cikin cunkoson jama'a yayin da shugaban gidan man AYM Shafa ke rabiyar Zakka.

Kara karanta wannan

N6bn: 'Yan APC a Kano sun taso Gwamna Abba a gaba kan kudaden ciyar da bayin Allah a Ramadana

Mata 4 sun mutu yayin karbar Zakka a jihar Bauchi
Aƙalla mata 4 ne suka mutu yayin karbar Zakka a jihar Bauchi a yau Lahadi. Hoto: Bala Mohammed.
Asali: Twitter

Yadda matan suka rasa rayukansu a Bauchi

Mata masu aure da marasa aure da matasa da kuma yara ne suka cika gidan mai din da ke kan hanyar Jos da safiyar yau Lahadi 24 ga watan Maris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun tabbatar da cewa da farko an fara rabiyar ba tare da matsala ba yayin ake kiransu daya bayan daya domin su karbi zakkar.

Daga bisani wasu daga ciki su ka gaza hakuri inda suka nemi shiga cikin harabar da ake rabiyar karfi da yaji wanda ya yi sanadin cunkoson.

Martanin rundunar 'yan sanda kan lamarin

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, SP Ahmed Wakili ya tabbatar da faruwar hakan ga 'yan jaridu, cewar Leadership.

Wakili ya ce sun samu kiran gaggawa cewar an kwashi mutane zuwa asibitin koyarwa na Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa.

Kara karanta wannan

Sokoto: An barke da murna yayin da almajirai 15 da aka sace suka kubuce daga miyagu

Daga bisani wasu daga ciki su ka gaza hakuri inda suka nemi shiga cikin harabar da ake rabiyar karfi da yaji wanda ya yi sanadin cunkoson.

"Zuwan jami'anmu ke da wuya suka taimaka wurin daukar marasa lafiyar zuwa asibiti."
"Sannan likita a asibitin ya tabbatar da mutuwar mata hudu inda wasu ke karbar kulawa ciki har da budurwa 'yar shekara 17."

- Ahmed Wakili

Wakili ya ce rundunar ta na rokon al'umma da su tabbatar sun gayyace ta domin tabbatar da tsari a rabo irin wannan ganin yadda ake cikin halin kunci a kasar.

Dalibai sun mutu kan rabon abinci

Kun ji cewa akalla dalibai biyu ne suka mutu yayin karbar rabin abinci a jihar Nasarawa da ke Arewacin Najeriya.

Lamarin ya faru ne a harabar Jami'ar jihar Nasarawa da ke Keffi yayin ake rabon kayan abincin domin rage radadin halin da ake ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel