Shahararren Mawaki a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Yau Juma’a

Shahararren Mawaki a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Yau Juma’a

  • An shiga jimami bayan rasuwar fitaccen mawaki a Najeriya, Godwin Opara wanda ya rasu da shekaru 77
  • Marigayin wanda aka fi sani da Kabaka ya yi bankwana da duniya ne a yau Juma'a 22 ga watan Maris
  • Mawakin ya shafe fiye da shekaru 20 ya na wakar gargajiya da kayan kida da zamani wanda ya yi kaurin suna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Imo - Shahararren mawaki a Najeriya, Godwin Opara ya riga mu gidan gaskiya ya na da shekaru 77 a duniya.

Marigayin wanda aka fi sani da ‘Kabaka’ ya rasu ne a yau Juma’a 22 ga watan Maris kamar yadda masu kula da wakokinsa suka tabbatar.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe sabon ango a harin kasuwar Arewa, an samu karin bayani

Mawaki Kabaka ya riga mu gidan gaskiya a Najeriya
Fitaccen mawakin, Kabaka ya rasu da shekaru 77 a duniya. Hoto: Godwin Opara.
Asali: Facebook

Shekaru nawa Opara ya yi yana waka?

Opara ya shafe fiye da shekaru 20 ya na waka da ta kunshi wake-waken gargajiya da amfani da kayan kidan zamani, a cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ammarachi Anyanwu, wacce ke kula wakokinsa a kamfanin Derda Promotions ita ta tabbatar da haka a yau Juma’a 22 ga watan Maris.

“Kabaka ya kasance kwararre kuma wanda mutane da dama ke son shi saboda irin kalar wakokin da ya ke yi.”

- Ammarachi Anyanwu

Sai dai Ammarachi ba ta bayyana karara dalilin mutuwar fitaccen mawakin ba yayin fitar da sanarwar, a cewar Premium Times.

A watan Satumbar 2023, tare da gudunmawar Derda Promotions, Kabaka ya fitar da wakarsa ta karshe mai suna ‘The Return of Kabaka”.

Wakar ta yi kaurin suna inda ta samu fiye da mutane miliyan daya da suka kalla kuma ta kasance daga cikin wakoki 100 fitattu.

Kara karanta wannan

Ana sa ran naira za ta mike, CBN ya biya bashin Dala biliyan 7 da Emefiele ya bari

Jarumin fina-finan Nollywood ya rasu

A wani labarin kuma, fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, Jimi Solanke ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayin ya rasu ne bayan ya sha fama da jinya na tsawon lokaci a birnin Abeokuta a jihar Ogun.

Solanke ya rasu ne yayin da aka dauke shi daga kauyensu a karamar hukumar Remo zuwa asibiti.

Mawaki Iriferi ya kwanta dama

Kun ji cewa, Fitaccen mawakin Urhobo a Najeriya, Cif Daniel Iriferi ya riga mu gidan gaskiya da shekaru 91.

Marigayin wanda aka fi sani da Sally Young ya mutu ne a ranar Litinin 12 ga watan Faburairu bayan fama da jinya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel