Kwankwaso Ya Yi Magana kan Kisan Gilla da Aka Yi wa Sheikh Masussuka a Katsina

Kwankwaso Ya Yi Magana kan Kisan Gilla da Aka Yi wa Sheikh Masussuka a Katsina

  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi alhinin rasuwar Sheikh Yahaya Masussuka wanda aka hallaka a Katsina
  • Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na NDC ya buƙaci gwamnati ta ɗauki matakan gaggawa domin kawo ƙarshen rashin tsaro a faɗin Najeriya
  • Tsohon gwamnan Kano ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, ɗalibansa da Musulmi, yana mai jaddada muhimmancin kare rayuka da dawo da zaman lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi martani kan kisan Sheikh Yahaya Masussuka.

Kwankwaso ya bayyana alhininsa kan rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Masussuka da yan bindiga suka kashe.

Kwankwaso ya yi jimamin kisan Masussuka
Marigayi Shiekh Ibrahim Yahaya Masussuka, Rabiu Musa Kwankwaso. Hoto: Shiekh Ibrahim Yahaya Masussuka, Rabiu Musa Kwankwaso.
Source: Facebook

Sanata Kwankwaso ya bayyana haka ne a cikin wani sakon ta'aziyya da ya wallafa a shafinsa na X a yau Talata 27 ga watan Oktobar 2026.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kama ɗan agajin Izala kan zargin barazana ga Kiristoci a bidiyo

Kwankwaso ya magantu kan kisan Masussuka

Kwankwaso ya yi Allah-wadai da kashe-kashen malaman addini da sauran fararen hula da ’yan bindiga ke yi, yana mai cewa lamarin ya zama babban abin damuwa da ke buƙatar ɗaukar matakan gaggawa.

Ya bayyana cewa kai hare-hare kan malaman addini abin takaici ne, musamman idan aka yi la’akari da gudummawarsu wajen yaɗa koyarwar Musulunci, kyawawan ɗabi’u, zaman lafiya da bunƙasa ruhaniya.

Sanarwar ta ce:

"Ina matuƙar alhini bisa rasuwar Sheikh Yahaya Masussuka, wadda ta ƙara jefa al’umma cikin damuwa game da yawaitar hare-hare da kashe malaman addini da sauran bayin Allah da ’yan bindiga ke yi a cikin al’ummarmu.
Abin damuwa ne matuƙa yadda ake ci gaba da kai hare-hare kan malaman addini, ganin irin muhimmiyar rawar da suke takawa wajen yaɗa koyarwar Musulunci, kyawawan ɗabi’u, zaman lafiya da jituwa, da bunƙasa rayuwar ruhaniya a cikin al’ummominmu."
Kwankwaso ya magantu kan kisan Masussuka
Tsohon gwamnan Kano, Rabi'u Kwankwaso. Hoto: Rabi'u Musa Kwankwaso.
Source: Twitter

Bukatar Kwankwaso ga hukumomi

Kwankwaso ya yi kira ga gwamnati da ta ɗauki kwararan matakai domin kare rayukan jama’a, hukunta waɗanda suka aikata laifukan kisan kai da kuma tabbatar da zaman lafiya a ƙasar.

Kara karanta wannan

Masussuka: Shehu Sani ya faɗi 'dalilai' da ke jawo kisan malamai a Arewa

Haka kuma, Kwankwaso ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, ɗalibansa, abokan hulɗarsa da daukacin al’ummar Musulmi, yana mai bayyana rasuwar a matsayin babban rashi.

"Ina Allah-wadai da wannan ta’addanci na rashin hankali da ake yi wa ’yan ƙasa. Ci gaba da salwantar rayuka sakamakon rashin tsaro abu ne da ba za a amince da shi ba.
"Wannan ya nuna buƙatar ɗaukar matakan gaggawa da ƙarfi domin kare al’ummarmu, hukunta waɗanda suka aikata wannan aika-aika, da dawo da zaman lafiya da tsaro a faɗin ƙasar nan.
Ina miƙa saƙon ta’aziyyata ga iyalansa, ɗalibansa, abokan hulɗarsa da kuma daukacin al’ummar Musulmi bisa wannan babban rashi."

- Cewar Kwankwaso

Martanin Tinubu kan kisa Masussuka a Katsina

A wani labarin, mun ba ku labarin cewa shugaba Bola Tinubu ya yi Allah wadai da kisan fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka, da abokinsa, Adamu Abubakar.

Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan kisan malamin da abokinsa, tare da cafke waɗanda suka aikata laifin domin gurfanar da su.

Shugaban ƙasa ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, mabiyansu da al’ummar Katsina, tare da addu’ar Allah Ya jiƙansu, Ya kuma ba masu alhinin mutuwarsu haƙuri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.