Kudin Makamai: EFCC Ta Sake Gurfanar da Tsohon Shugaban PDP Bayan Sabunta Kara

Kudin Makamai: EFCC Ta Sake Gurfanar da Tsohon Shugaban PDP Bayan Sabunta Kara

  • Hukumar EFCC ta sake dawo da maganar karkatar da kudin makamai na zamanin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan
  • Hukumar ta sake gurfanar da tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Bello Halliru Mohammed kan zargin karkatar da N300m
  • Ana zargin Bello ne da dansa wanda yanzu ya rasu da kuma kamfaninsa kan badakalar kudade domin siyan makamai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Hukumar EFCC ta sake gurfanar da tsohon mukaddashin shugaban jam’iyyar PDP, Halliru Bello kan zargin badakala.

Hukumar na zargin Bello da hannu a karkatar da kudin makamai har N300m a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.

Tsohon shugaban PDP ya sake shiga matsala bayan EFCC ta gurfanar da shi a gaban kotu
Hukumar EFCC ta sake gurfanar da Haliru Bello kan badakalar makamai. Hoto: Haliru Bello Mohammed, Economic and Financial Crimes Commission.
Asali: Facebook

EFCC: Tun yaushe ake tuhumar Haliru Bello?

Kara karanta wannan

Ganduje ya dinke ɓarakar da ta kunno kai a APC, an sauya mataimakin dan takarar gwamna

Tun farko an gurfanar da Halliru Bello ne a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a shekarar 2016.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai an sabunta tuhumar inda a yau Litinin 18 ga watan Maris aka sake gurfanar da shi bayan shekaru takwas.

Ana zargin Bello da dansa wanda ya rasu da kuma wani kamfaninsa mai suna Bam Projects and Properties kan tuhume-tuhume guda hudu.

Tuhume-tuhumen sun hada da cin amana da badakalar kudi har N300m ta ofishin tsohon mai ba da shawara a harkokin tsaro, Sambo Dasuki.

Premium Times ta ruwaito cewa Dasuki ya yi aiki a matsayin mai ba tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan shawara kan tsaro.

Matakin da EFCC ta dauka kan shari'ar

Hukumar EFCC ta bakin lauyanta, Rotimi Jacobs ya sake shigar da kara bayan sabunta tuhumar a yau Litinin 18 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Rundunar soji ta saduda, ta nemi agajin EFCC a wasu bangarori, ta fadi dalili

Lauyan wanda ake zargi, Kanu Agabi ya tabbatar da samun takardar tuhumar wacce aka sabunta kan wanda ya ke karewa.

Sai dai wanda ake zargi ya musanta dukkan korafe-korafen da ake yi kansa yayin da lauyansa ya bukaci kotun ta ba Bello beli kamar yadda ya ke a baya.

Alkalin kotun daga bisani ya amince da bukatar lauyan inda ya ba shi damar ci gaba da zama kan sharadin belin da tsohon alkalin ya ba shi.

Dagan nan ne sai alkalin kotun ya dage ci gaba da sauraran karar har zuwa ranar 7 da kuma 8 ga watan Mayu, cewar Daily Post.

Yan bindiga sun hallaka dagaci a Bauchi

Kun ji cewa wasu ‘yan bindiga sun yi ajalin basarake a jihar Bauchi bayan sace shi a gidansa.

Marigayin Garba Badamasi shi ne dagacin Riruwai da ke karamar hukumar Toro a jihar Bauchi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel