Ana Daf da Gudanar da Zabe, Mai Neman Takarar Gwamnan APC Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Ana Daf da Gudanar da Zabe, Mai Neman Takarar Gwamnan APC Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Ana tsaka da shirye-shiryen gudanar da zaben fitar da gwani, mai neman takarar gwamnan APC, Paul Akintelure a Ondo ya rasu
  • Marigayin ya rasu ne da safiyar yau Talata 26 ga watan Maris yayin da ake daf da gudanar da zaben jihar a wannan shekara
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin jam'iyyar APC a jihar, Oladapo Akintelure ya fitar da safiyar yau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ondo - Mai neman tikitin zama gwamnan jihar Ondo a zaben 2024, Dakta Paul Akintelure ya riga mu gidan gaskiya.

Akintelure wanda yana harin takara a jam'iyyar APC a zaben da za a gudanar ya rasu ne a yau Talata 26 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Zaben Senegal: Dan shekara 44, Bassirou Faye, ya kafa tarihi a siyasar Afrika

Mai neman takarar gwamna a APC a Ondo ya rasu
Mai neman takarar gwamnan a APC, Paul Akintelure ya rasu ne a yau Talata. Hoto: Paul Akintelure.
Asali: Twitter

Yaushe marigayin ya rasu a Ondo?

Kakakin jam'iyyar APC a jihar, Alex Kalejaye shi ya tabbatar da haka ga gidan talabijin na Channels da safiyar yau Talata 26 ga watan Maris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Marigayin wanda likita ne da ya dawo dan siyasa, a baya, ya yi korafin yadda ake masa barazana da rayuwarsa ta bangarori da dama, cewar Vanguard.

Daktan ya tsaya takarar mataimakin gwamna a zaben 2012 a jam'iyyar ACN da marigayi tsohon gwamna Rotimi Akeredolu.

Jarumin fina-finan Nollywood ya rasu

Fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, Amaechi Muonagor ya kwanta dama ya na da shekaru 62 a duniya.

Rahotanni da aka yada a kafofin sadarwa sun tabbatar da mutuwar fitaccen jarumin a ranar Lahadi 24 ga watan Maris a jihar Anambra.

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan rasuwar wani jarumin mai suna John Okafor da aka fi sani da Mista Ibu bayan fama da jinya.

Kara karanta wannan

El-Rufai ya rikita komai yayin da yake ganawa da shugabannin APC da jam'iyyun adawa

Mawaki a Najeriya ya rasu

A baya, mun ruwaito cewa wani shahararren mawaki a Najeriya, Godwin Opara ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayin da aka fi sani da 'Kabaka' ya rasu ne bayan fama da jinya ya na da shekaru 77 a duniya.

Kabaka ya shafe shekaru fiye da 20 ya na waka da suka hada da na gargajiya wurin yin amfani da kayan kisan zamani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel