Abba Kabir Yusuf Ya Sanar da Rasuwar Babban Dan Kasuwa a Kano

Abba Kabir Yusuf Ya Sanar da Rasuwar Babban Dan Kasuwa a Kano

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana alhininsa kan rasuwar fitaccen ɗan kasuwa Alhaji Isma’il Mukhtar Maibiskit
  • Gwamnan ya ce rasuwar Maibiskit babban rashi ne ga jihar Kano, musamman ’yan kasuwa, saboda gudunmawar da ya bayar wajen bunƙasa harkokin kasuwanci
  • Abba Kabir Yusuf ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, tare da roƙon Allah ya gafarta masa kurakuransa, ya ba shi Aljannatul Firdaus

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kano – Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi jimamin rasuwar fitaccen ɗan kasuwa kuma jigo a masana’antu, Alhaji Isma’il Mukhtar Maibiskit, wanda ya rasu a ranar Juma’a.

Gwamnan ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga jihar Kano, musamman ga ’yan kasuwa, bisa la’akari da gudunmawar da marigayin ya bayar wajen bunƙasa kasuwanci da kamfanoni masu zaman kansu a jihar.

Kara karanta wannan

Ana son ba da diyyar N1.4bn ga iyalan masu hakar ma'adinan da aka kashe a Neja

Isma’il Mukhtar Maibiskit
Abba Kabir Yusuf ya ziyarci Isma’il Mukhtar Maibiskit a asibiti. Hoto: Sanusi Bature
Source: Facebook

Sanarwar da kakakin gwamnatin Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a Facebook a ranar 30 ga Oktoba, 2026, ta bayyana cewa gwamnan ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin.

Gudunmawar Maibiskit a Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa marigayin na cikin fitattun ’yan kasuwar da suka bayar da gagarumar gudunmawa wajen bunƙasa harkokin kasuwanci a jihar Kano.

Ya ce ƙoƙarin Maibiskit ya taimaka wajen ƙarfafa matsayin Kano a matsayin ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin kasuwanci da masana’antu a Najeriya.

Gwamnan ya jaddada cewa rasuwarsa babban rashi ne ga ’yan kasuwa da sauran al’ummar jihar da suka amfana da gudunmawarsa.

Abba ya yi ta’aziyyar Maibiskit

A cikin saƙon ta’aziyyarsa, Abba Yusuf ya miƙa sakon jaje ga iyalan marigayin, musamman jikarsa, Injiniya Yasmin Mukhtar, wadda ke riƙe da muƙamin babbar mataimakiya ta musamman ga gwamnan kan ilimin mata.

Ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga sauran ’yan uwa, abokai, abokan hulɗar kasuwanci da al’ummar jihar Kano baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kama ɗan agajin Izala kan zargin barazana ga Kiristoci a bidiyo

Gwamnan ya shawarci iyalan da su yi haƙuri tare da tunawa da kyawawan ayyuka da tarihin rayuwar marigayin.

Abba Kabir Yusuf ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki da ya gafarta wa marigayin kurakuransa, ya karɓi kyawawan ayyukansa, ya kuma saka masa da Aljannatul Firdaus.

Taswirar jihar Kano
Taswirar jihar Kano a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Haka kuma, ya yi addu’ar Allah ya ba iyalansa da duk waɗanda rasuwar ta shafa haƙurin jure wannan babban rashi.

An kara yawan sojoji a Kano

A wani labarin, kun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta tura sabuwar bataliya da rundunar manyan makamai zuwa jihar domin ƙarfafa tsaro da inganta martanin jami’an tsaro ga barazanar da ka iya tasowa.

Kwamandan rundunar soji ta 1 kuma kwamandan ɓangare na 1 na Operation Fansan Yamma, Manjo Janar Abubakar Muhammad Wase, ya bayyana cewa rundunonin na buƙatar jajircewa, juriyar aiki da cikakken goyon baya.

Wase ya bayyana hakan ne yayin ziyarar tantance ayyukan soji da ya kai bataliya ta 24 da ke Tudun Wada da rundunar manyan makamai ta 311 da ke Dambatta, tsakanin ranakun 28 da 29 ga Oktoba, 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng