Fitaccen Jarumi Ya Fadi Yadda Ya Watsar da Musulunci da Kiristanci Bayan Dogon Nazari

Fitaccen Jarumi Ya Fadi Yadda Ya Watsar da Musulunci da Kiristanci Bayan Dogon Nazari

  • Ɗan wasan kwaikwayo a Najeriya, Debo Adebayo ya bayyana yadda ya ke gudanar da rayuwarsa ba tare da addini ba
  • Jarumai fina-finan wanda aka fi sani da Mr Macaroni ya ce yanzu haka duk ya watsar da addinan Musulunci da Kiristanci
  • Jarumin ya bayyana haka ne yayin hira da Biola Bayo wanda ya wallafa faifan bidiyon a shafinsa na Instagram

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Legas - Jarumin fina-finai, Debo Adebayo ya bayyana yadda ya yi addinai biyu a rayuwarsa kafin daga bisani ya watsar da dukkansu.

Jarumin wanda aka fi sani Mr Macaroni ya ce a yanzu ba ya cikin kowane addini da ake da su a Najeriya kuma ya na jin dadin rayuwarsa.

Kara karanta wannan

Sarki Charles III ya yi bankwana da duniya? Gaskiya ta bayyana

Jarumin fina-finai ya magantu kan rayuwarsa a Musulunci da kuma kiristanci
Mr Macaroni ya ce a yanzu ba ya bin addinin Musulunci ko na Kiristanci. Hoto: @mrmacaroni1.
Asali: Instagram

Binciken Macaroni kan kiristanci da musulunci

Macaroni ya bayyana cewa mahaifinsa Musulmi ne yayin da mahaifiyarsa kuma ta kasance Kirista.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adebayo ya ce ya yi bincike mai zurfi kan dukkan addinan biyu amma yanzu duk ya watsar da su.

Ya ce a duk lokacin da ya tashi ya na mika lamuransa ga Ubangiji ne sannan ya yi iya bakin kokarinsa.

Mr. Macaroni ya yi magana kan daukakarsa

Jarumin ya bayyana haka ne yayin da ya wallafa wani faifan bidiyo a Instagram inda ya yabawa 'yan Najeriya kan yadda su ke da juriya a wannan hali da ake ciki.

A cikin hirar da ya yi da Biola Bayo, Macaroni ya ce tun farko ya sani zai zama fitacce a duniya.

Ya ce ya san mutane da yawa wadanda basu yin wani addini amma kuma sun ci gaba a rayuwarsu ta kowane fuska.

Kara karanta wannan

Ramadan: Dan takarar shugaban kasa na LP ya ziyarci Musulmi an yi buda baki da shi

Jaruma ta shawarci ma'aurata

Kun ji cewa jarumar fina-finai Nollywood, Tosin Adekinsola ta shawarci ma'aurata kan saduwa da juna kafin su kai ga yin aure.

Jarumar ta ce hakan ya na kara dankon soyayya da zumunci wanda zai yi wahala a samu matsala daga baya.

Tosin ta ce amfanin hakan shi ne kowa zai san dan uwansa tun kafin a shiga daga ciki wanda zama ne na din-din-din.

Asali: Legit.ng

Online view pixel