Bayan Kisan Sojoji 16, an Bankawa Kauyen da Abin Ya Faru Wuta, Bayanai Sun Fito

Bayan Kisan Sojoji 16, an Bankawa Kauyen da Abin Ya Faru Wuta, Bayanai Sun Fito

  • Rahotannin da muke samu yanzu sun tabbatar de cewa an kona kauyen Okuama da ke karamar hukumar Ughelli ta Kudu
  • Kauyen Okuama nan ne ake zargin wasu bata gari sun hallaka manyan jami'an sojoji 16 yayin fadan kabilanci a yankin
  • Rundunar sojin daga bisani da tabbatar da cafke wasu mutane da ake zargin da hannunsu a kisan jami'an sojin a ranar Alhamis

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Delta - An bankawa kauyen da ake zargin an hallaka wasu manyan sojoji 16 a jihar Delta.

Lamarin ya faru ne a kauyen Okuama da ke karamar hukumar Ughelli ta Kudu a jihar bayan hallaka sojoji 16 a ranar Alhamis 14 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Gaza: Bam ya kashe ‘yanuwa 36 lokacin shirin sahur a dauki azumin Ramadan

An kona kauyen da aka yi wa sojoji kisan gilla kurmus da safiyar yau
Ana zargin wasu sojoji sun kona kauyen da aka hallaka sojoji 16. Hoto: Nigerian Army, Channels TV.
Asali: Facebook

Nasarar da rundunar ta samu bayan harin

An zargin fusatattun sojojin ne suka dauki wannan matakin bayan kisan 'yan uwan nasu, Channels TV ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, rundunar sojin ta tabbatar da kama wasu da ake zargi da hannunsu a kisan bayan umarnin fara bincike kan lamarin.

Rahotanni sun tabbatar da cewa al'ummar yankin sun tsere zuwa garuruwa makwabta saboda tsoron daukar mataki daga sojoji, cewar Premium Times.

Umarnin da rundunar ta bayar ga sojoji

Daraktan yada labaran rundunar, Burgediya-janar Tukur Gusau ya ce hafsan tsaron kasar, Janar Christopher Musa ya ba da umarni bincike da kama wadanda ake da hannu a kisan.

Tukur ya bayyanawa Legit cewa bayan umarnin Janar Musa sun kuma sanarwa gwamnatin jihar Delta faruwar lamarin a hukumance.

Har ila yau, gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwore ya yi Allah wadai da kisan sojojin a jiharsa inda ya tura sakon ta'aziyya.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Rundunar soji ta saduda, ta nemi agajin EFCC a wasu bangarori, ta fadi dalili

An halllaka sojoji 16 a Delta

Kun ji cewa sojoji akalla 16 ne wasu bar gari a jauyen Okuoma suka halaka a karamar hukumar Ughelli ta Kudu a jihar Delta.

Rahotanni sun tabbatar da cewa sojojin na Bataliya ta 181, Bomadi, sun je aikin ceto ne a lokacin da maharan suka yi musu kwanton ɓauna a ranar Alhamis 14 ga watan Maris.

Daga bisani an tabbatar da cewa an cafke wasu mutane da ake zargin da hannunsu a cikin kisan gillar da aka yi wa sojojin a jihar Delta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel