Innalillahi: Mummunar Gobara Ta Laƙume Kadarori a Babbar Kasuwar Sokoto, Akwai Bayanai

Innalillahi: Mummunar Gobara Ta Laƙume Kadarori a Babbar Kasuwar Sokoto, Akwai Bayanai

  • An shiga wani irin yanayi bayan mummunar gobara ta tashi a babbar kasuwa a jihar Sokoto da safiyar yau Litinin
  • Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa gobarar ta kona babura da dama a kasuwar wanda yanzu ba a san adadinsu ba
  • Shugaban masu siyar da babura, Shehu Muhammad ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce an tafka asara sosai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Sokoto - Rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa mummunar gobara ta kama babbar kasuwa a jihar Sokoto.

Mummunar gobarar ta yi barna musamman bangaren babura wanda ta kone su kurmus da kuma wasu shaguna, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ba da sabon umarni ga rundunar tsaro bayan kisan sojoji 16, ya yi Allah wadai

Gobara da tafka asara a babbar kasuwar jihar Sokoto
Mummunar gobara ta jawo asara a babbar kasuwar jihar Sokoto. Hoto: Ahmed Aliyu.
Asali: Twitter

Yaushe gobarar ta tashi a kasuwar Sokoto?

Wani shaidan gani da ido ya fadawa Punch cewa gobarar ta fara ne da safiyar yau Litinin 18 ga watan Maris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyar ta ce har zuwa yanzu ba za a iya tantance musabbabin gobarar da ta lalata duniyoyin jama'a ba.

Har ila yau, wata majiya ta daban ta tabbatar da cewa ana zargin gobarar ta fara ne daga wata bola da ke kusa da bangaren da baburan suke.

Shugaban kungiyar masu siyar da baburan, Shehu Muhammad ya ce ba za su iya sanin adadin asarar da aka yi ba tun da har yanzu wutar na ci.

Gobara: Martanin shugaban masu siyar da babura

"Ba za mu iya sanin adadin babura da suka kone ba saboda har yanzu wutar ta na ci."
"Mutane da dama sun rasa shagunansu da babura saboda ba su samu zuwa kasuwa da wuri saboda wutar ta fara tun shida na safe."

Kara karanta wannan

Gwamna ya fadi halin kunci da ya ke ciki, ya ce shekaru 2 bai samu albashi ba, ya yi tone-tone

"Jami'an kashe gobara su na iya bakin kokarinsu amma na san zai dauki lokaci kafin dakile wutar gaba daya."

- Shehu Muhammad

Shehu ya roki gwamnati ta kawo dauki musamman ga wadanda suka tafka asarar dukiyoyi yayin iftila'in gobarar, cewar PM News.

Gwamna Ahmed ya gwangwaje ma'aikata

Kun ji cewa gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya gwangwaje ma'aikata da rabin albashinsu kyauta.

Aliyu ya dauki wannan matakin ne domin tabbatar da ma'aikatan jihar sun gudanar azumin watan Ramadan cikin walwala.

Wannan na zuwa ne yayin da ake fama da matsanancin tsadar kayan abinci a fadin kasar baki daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel