Shugaban Karamar Hukuma Ya Ci Mutuncin Malami da Ya Saka Rigar Dan Adawarsa

Shugaban Karamar Hukuma Ya Ci Mutuncin Malami da Ya Saka Rigar Dan Adawarsa

  • Isah Baba Bida, shugaban karamar hukumar Katcha a Neja, ya fuskanci suka bayan wani bidiyo na cin mutuncin malami
  • Shugaban ya umarci malamin ya cire rigar mai ɗauke da hoton ɗan takarar PDP, Mohammed Nami, tare da rubuta sunansa
  • Malamin ya musanta ikirarin cewa ɗalibai biyu ne kawai a makarantar, inda ya ce tana da sama da ɗalibai 200

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Katcha, Niger - Shugaban karamar hukumar Katcha da ke jihar Neja, Isah Baba Bida, ya shiga cikin ce-ce-ku-ce bayan cin mutuncin malamin makaranta.

Wani bidiyo ya bayyana a kafafen sada zumunta yana yi wa wani malami faɗa kan sanya rigar da ke ɗauke da hoton ɗan siyasa mai hamayya da gwamnati.

An soki ciyaman kan cin mutuncin malami saboda siyasa
Shugaban karamar hukumar Katcha, Isah Baba Bida da malamin makaranta. Hoto: Sahara TV.
Source: Facebook

Rahoton Daily Trust ya ce shugaban ya kai ziyara makarantar ne a safiyar ranar Litinin, inda ya nuna rashin jin daɗinsa kan irin tufafin da malamin ya sanya.

Kara karanta wannan

Matasa sun shiga babbar matsala da suka jefi magoya bayan APC a tawagar gwamna

Bidiyon ya nuna shugaban karamar hukumar yana takaddama da malamin, Yahaya Mohammed Sakiwa, a makarantar firamare ta Kafa, inda ya umarce shi da ya cire rigar tare da rubuta sunansa.

Dalilin shugaban na yi wa malamin faɗa

A cikin bidiyon da ya yaɗu da aka samu a Youtube, Bida ya ce ya je makarantar ne domin samun sahihin bayani kan malaman da ke sanya rigunan da ke ɗauke da sunan ɗan takarar gwamnan PDP a jihar Neja, Mohammed Nami.

Ya umarci Sakiwa da ya cire rigar tare da rubuta sunansa da sunayen sauran ma’aikatan makarantar da ba su halarta ba.

Shugaban ya ce:

“Ina da sha’awa ta musamman a wannan makarantar firamare, wa ya umarce ka da ka sanya wannan kayan? Malami yana sanya kayan jam’iyyar adawa. Ka rubuta sunanka da sunayen sauran ma’aikatan da ba su zo ba, sannan ka cire wannan rigar.”

Kara karanta wannan

Atiku ya zargi Tinubu da shirin tafiya Faransa amma ya fake da zuwa Saudi

Bida ya kuma nuna damuwarsa kan lalacewar makarantar da kuma ƙarancin ɗaliban da ya tarar a lokacin da ya isa wurin.

Ya ce ya tarar da malami guda ɗaya da ɗalibai biyu, waɗanda a cewarsa ba su san sunan makarantar ko sunayensu ba.

An yi ta ce-ce-ku-ce da ciyaman ya ci mutuncin malami
Taswirar jihar Niger da APC ke mulki. Hoto: Legit.
Source: Original

Malamin ya musanta ikirarin ciyaman

Sakiwa, wanda malami ne na wucin gadi a makarantar, ya ce shugaban karamar hukumar ya tuntubi shi da baffanninsa domin neman afuwa kan abin da ya faru.

Sai dai malamin ya musanta ikirarin cewa ɗalibai biyu ne kawai suka kasance a makarantar lokacin ziyarar shugaban.

Ya ce makarantar tana da ɗalibai sama da 200, kuma shugaban ya isa ne da sassafe lokacin da yara ke fara zuwa makaranta.

Sakiwa ya ce:

“Abin da shugaban ya fada cewa babu ɗalibai a makarantar ba gaskiya ba ne. Ya zo da safe ne lokacin da yara suka fara zuwa makaranta.

Ƙungiyar Malamai ta NUT ta yi gargadi

A nata martanin, ƙungiyar malaman Najeriya (NUT) reshen jihar Neja ta ja kunnen malamai kan shiga harkokin siyasa ta bangaren nuna goyon bayan jam’iyya.

Kara karanta wannan

Tallafin mai: ADC ta sake albishir ga Ƴan Najeriya kan shirin Atiku bayan hawa mulki

A cikin wata sanarwa da sakataren ƙungiyar na jihar, Umaru Musa Kuta, ya fitar, NUT ta ce ta amince malamai suna da ’yancin ra’ayin siyasa bisa kundin tsarin mulki.

An kusa lakadawa ciyaman duka a Neja

A baya, an ji cewa rigima ta kaure tsakanin magoya bayan APC da shugabanni a Neja kan zaɓen ƴan takararar da za su fafata a zaɓen kananan hukumomi.

Ƴan jam'iyyar APC sun fara zargin ana neman tursasa su wajen tsayar da ƴan takara bisa tsarin da Gwamna Umaru Bago ya kawo.

Zanga-zanga ta zama rigima a sakatariyar APC a ƙaramar hukumar Agwara, haka nan matasa sun gargaɗi Gwamna ya sauka daga tsarinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.