An Sake Shiga Jimami Bayan Fitaccen Jarumin Fina-finai Ya Kwanta Dama

An Sake Shiga Jimami Bayan Fitaccen Jarumin Fina-finai Ya Kwanta Dama

  • Masana'antar Nollywood ta sake babban rashi bayan mutuwar shahararren jaruminta mai suna Amaechi Muonagor
  • Marigayin ya mutu ne a yau Lahadi 24 ga watan Maris bayan ya sha fama da jinyar cutar hanta na tsawon lokaci
  • Mutuwar Amaechi na zuwa ne kwanaki kadan bayan jarumin fina-finan, John Okafor wanda aka fi sani da Mista Ibu ya mutu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Anambra - Fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, Amaechi Muonagor ya kwanta dama.

Rahotanni da aka yada a kafofin sadarwa sun tabbatar da mutuwar fitaccen jarumin a yau Lahadi 24 ga watan Maris.

Jarumin fina-finai ya riga mu gidan gaskiya
Amaechi Muonagor ya rasu ne a yau Lahadi bayan fama da jinya. Hoto: Amaechi Muonagor.
Asali: Instagram

Wahalar da marigayin ya shiga kafin rasuwarsa

Kara karanta wannan

Abacha ya karkatar da maƙudan kudi a mulkinsa? Buba Galadima ya fayyace gaskiya

Marigayin ya sha fama da jinya na tsawon lokacin inda ya nemi taimako a faifan bidiyo domin yi masa aiki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Marigayin ya sha fama da cutar hanta wanda ta yi sanadin karewar dukkan abin da ya mallaka har ya fara neman taimako, cewar Pulse.

Sai har yanzu kungiyar jaruman fim ta kasa (AGN) ko iyalansa ba su yi magana kan mutuwar tashi ba.

An haifi jarumi Muonagor a ranar 20 ga watan Agustan 1962 a karamar hukumar Idemili a jihar Anambra.

A shekarar 1989 marigayin ya fara aiki da New Agency of Nigeria (NAN) kafin daga bisani ya koma harkar fina-finai, kamar yadda Punch ta tattaro.

Mista Ibu ya riga mu gidan gaskiya

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan mutuwar fitaccen jarumi, John Okafor wanda aka fi sani da Mista Ibu.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya karyata masu jita-jita cewa ya ware N6bn don ciyar da Kanawa a Ramadana

Mista Ibu shi ma ya sha fama da jinya wanda har ta yi sanadin yanke masa kafa kafin rasuwar ta shi.

Mutuwar marigayin ya rikita masoya kallon fina-finan Nollywood daga dukkan bangaren kasar Najeriya baki daya saboda yadda ya yi kaurin suna.

Mawaki Opara ya riga mu gidan gaskiya

Kun ji cewa shahararren mawaki a Najeriya, Godwin Opara ya kwanta dama ya na da shekaru 77 a duniya.

Marigayin ya shafe fiye da shekaru 20 ya na wakoki a Najeriya inda ya ke wakokin gargajiya da kuma amfani da kayan kisan zamani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel