Abun Bakin Ciki
Zuciyar wani mutumi ya karaya bayan ya gano cewa ba shine uban ‘yarsa ba. Ya yi shirin mayar da ita kasar Amurka ne lokacin da ya gano gaskiya a kanta.
Kamfanin BUA ya tafka asara yayin da jama'a suka tare motarsa a Zariya suka wawushe gaba daya katan-katan na taliyar da ta dauko a dai dai garin Dogarawa.
Yayin da ‘yan Najeriya ke kokawa kan farashin siminti a kasar, kamfanin Dangote ya sanar da kazamar ribar da ya samu a bangaren a karshen shekarar 2023.
Rundunar sojin Najeriya ta gargadi Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Igboho kan irin kalaman da ya ke yi tun bayan dawowa Najeriya a ranar 22 ga watan Faburairu.
Wata karamar yarinya ta mutu yayin da aka kwantar da mutum hudu a asibitin koyarwa na LAUTECH, bayan cin tuwon alabo a yankin Temidire Atoyebi da ke Oyo.
Shugaban hukumar Hisbah, Sheikh Ibrahim Aminu Daurawa ya yi murabus daga kujerarsa inda ya ce bai ji dadin maganganun da suka fito daga jihar Kano ba.
A ranar Alhamis ne wani Adebayo Olamide Azeez, ya bayyana yadda ya yaudari wasu mata 7 ta hanyar amfani da manhajar "MyChat" inda ya kashe su domin yin tsafi.
Majalisar zartarwa a Najeriya ta yi alhinin mutuwar tsohon Ministan ilimi a mulkin Cif Olusegun Obasanjo, Farfesa Fabian Osuji a yau Alhamis 29 ga watan Faburairu.
Mai gwagwarmayar kafa kasar Yarbawa, Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho ya shiga matsala kan gargadin da kungiyar Yarbawa ta yi masa.
Abun Bakin Ciki
Samu kari