Dara Za Ta Ci Gida Yayin da Yarbawa Suka Tura Gargadi Ga Igboho Kan Wani Dalili, Mun Samu Bayanai

Dara Za Ta Ci Gida Yayin da Yarbawa Suka Tura Gargadi Ga Igboho Kan Wani Dalili, Mun Samu Bayanai

  • Yayin da mai gwagwarmayar kafa kasar Yarbawa ya dawo Najeriya don bikin binne mahaifiyarsa, an tura masa gargadi
  • Kungiyar Yarbawa ta gargadi Sunday Igboho da ya kula da kalaman da ya ke yi da mabiyansa kan dattawan yankin Yarbawa
  • Shugaban kungiyar, Cif Onitolo-Ariyo Adejare shi ya bayyana haka a jiya Laraba 28 ga watan Faburairun wannan shekara

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Kungiyar Yarbawa ta tura sakon gargadi ga mai fafutukar kafa kasar Yarbawa, Sunday Adeyemo kan kalamansa na ta da husuma.

Kungiyar mai suna Yoruba Alliance Forum, YAF ta yi gargadin ne ga Igboho kan cin mutuncin dattawan yankin Yarbawa.

Igboho ya same burma wa matsala kan kalamansa a yankin Yarbawa
Kungiyar Yarbawa ta gargadi Igboho kan munanan kalamansa kan dattawan yankin. Hoto: Sunday Adeyemo.
Asali: Twitter

Wane gargadi kungiyar ta yi wa Igboho?

Kara karanta wannan

Duk da durkusar da Najeriya, an bayyana Emefiele a matsayin mafi kwarewa a CBN, akwai dalilai

Ta ce bai kamata a saka masa ido magoya bayansa su na cin mutuncin mutanen da suka sadaukar da rayuwarsu wurin ci gaban yankin ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kungiyar, Cif Onitolo-Ariyo Adejare shi ya bayyana haka a jiya Laraba 28 ga watan Faburairu, cewar Tribune.

Kungiyar ta yi martanin ne bayan cin mutuncin dattawan da Igboho ke yi a kafafen yada labarai inda suka ce ya bai san menene gwamarmaya ba tukuna.

Ta bai wa dan gwagwarmayar shawara

Ta ce daga cikin wadanda ya ke zargin akwai cif-cif da Obas na yankin da Aare Onakakanfo da kuma Gani Adams, kamar yadda Newshour ta tattaro.

Ta kuma bukace shi da ya san menene gwamarmaya da koyan darasi inda suka ce Kabilar Yarbawa ta fi ko wace tsari a duniya.

YAF ta ce ta na bibiyar dukkan takun Igboho inda ta ce tun bayan da ya dawo Najeriya bikin binne mahaifiyarsa da alamu bai koyi darasi ba.

Kara karanta wannan

Fitaccen basarake a Arewa ya magantu kan halin kunci, ya tura sako ga 'yan kasuwa kan tsadar kaya

Igboho ya yi martani ga Sultan

A baya, kun ji cewa dan gwagwarmayar kafa kasar Yarbawa, Sunday Adeyemo ya yi martani ga Mai Martaba Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar.

Adeyemo wanda aka fi sani da Igboho ya yi martanin ne kan kalaman Sarkin Musulmi inda ya ce lamarin kasar ya gama lalacewa.

Igboho ya ce wannan matsala ba laifin gwamnatin Tinubu ba ne don shi ma a haka ya same ta tun da bai wuce watanni takwas ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel