Bayan Mutuwar Mista Ibu, Wata Shahararriyar Jarumar Fina-Finai a Najeriya Ta Tafka Babban Rashi

Bayan Mutuwar Mista Ibu, Wata Shahararriyar Jarumar Fina-Finai a Najeriya Ta Tafka Babban Rashi

  • Masana’antar Nollywood ta sake shiga jimami bayan rasuwar mahaifiyar daya daga cikin fitattun jarumanta, Kate Henshaw
  • Shugaban kungiyar jaruman (AGN), Emeka Rollas shi ya bayyana rasuwar marigayiyar a jiya Asabar 2 ga watan Maris
  • Wannan na zuwa ne bayan sanar da rasuwar fitaccen jarumin fina-finai, John Okafor da aka fi sani da Mista Ibu a jiya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Legas - Awanni kadan bayan sanar da mutuwar jarumin fina-finan Nollywood, Mista Ibu, wata jaruma a masana’antar ta sake rasa mahaifiyarta.

Fitacciyar jarumar fina-finan Nollywood, Kate Henshaw ta rasa mahaifiyar tata ne bayan dattijuwar ta sha fama da jinya.

Mahaifiyar jarumar fina-finai a Najeriya ta riga mu gidan gaskiya
Kate Henshaw ta rasa mahaifiyarta a jiya Asabar. Hoto: @k8henshaw.
Asali: Instagram

Yaushe aka sanar da mutuwar marigayiyar?

Kara karanta wannan

Fitaccen jarumin fina-finai a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya da shekaru 62, bayanai sun fito

Shugaban kungiyar jaruman (AGN), Emeka Rollas shi ya bayyana rasuwar marigayiyar a shafin Instagram a jiya Asabar 2 ga watan Maris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rollas yayin tabbatar da mutuwar dattijuwar, ya mika sakon jaje ga iyalan marigayiyar da kuma ita kanta Kenshaw.

Shugaban ya kuma bayyana mutuwar matar a matsayin abin bakin ciki musamman ga kungiyar tasu ta jarumai.

A cewarsa:

“Wannan rana ce ta bakin ciki a kungiyarmu, Kate Henshaw ta rasa mahaifiyarta da safiyar yau.”

Shurar da jaruma Henshaw ta yi

Jarumar, Henshaw ta kasance mai magana da yawun kungiyar ta jaruman wacce ta yi kaurin suna a masana’antar.

Kate ta tsunduma harkar fina-finai fiye da shekaru 20 wanda ta fito a fina-finai da dama wanda ta taka rawar gani.

Jarumar ta yi kaurin suna ne a wani fim da ta fito tun a shekarar 1993 mai suna “When sun sets”.

Kara karanta wannan

Kungiyar Fulani ta Miyetti Allah ta nemi a kame dan fafutukar raba Najeriya gida biyu

Har ila yau, fitaccen jarumin fina-finan Yarbanci, Quadri Sisi ya riga mu gidan gaskiya a ranar Juma’a 1 ga watan Maris.

Mista Ibu ya riga mu gidan gaskiya

Mun ruwaito muku cewa masana’antar Nollywood ta yi babban rashi bayan mutuwar jaruminta, John Okafor.

Marigayin wanda aka fi sani da Mista Ibu ya rasu ne a jiya Asabar 2 ga watan Maris ya na da shekaru 62 a duniya.

Idan ba amanta ba a kwanakin baya likitoci dole suka yanke masa kafa don ceto rayuwarsa bayan taimakon da ya samu daga jama’a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel