Bayan Bude Masallaci da Aka Rufe Shekaru 5, Malamai Sun Gargadi Gwamnan PDP Kan limami

Bayan Bude Masallaci da Aka Rufe Shekaru 5, Malamai Sun Gargadi Gwamnan PDP Kan limami

  • Kungiyar malaman Musulunci a garin Inisa da ke jihar Osun sun shawarci Gwamna Ademola Adeleke kan shiga lamarin zaben limami
  • Gamayyar malaman ta bukaci gwamnan da ya tsame hannunsa kan lamarin dauko sabon limamin babban masallacin Inisa a jihar
  • Wannan na zuwa ne yayin da aka sake bude masallacin a watan Disamba bayan ya shafe kusan shekaru biyar a kulle kan rikici

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Osun – Gamayyar malaman addinin Musulunci a kauyen Inisa da ke jihar Osun sun shawarci gwamnan jihar kan zaban limami.

Malaman sun kuma gargadi Gwamna Ademola Adeleke kan kakaba musu wani limami na babban masallacin Inisa.

Malaman Musulunci sun roki gwamnan PDP ya cire hannunsa kan zaban liman
An rufe masallaci a kan rikicin limami. Hoto: Ademola Adeleke, Abdulrasaq Amad.
Asali: Facebook

Wane gargadi malaman suka yi?

Kara karanta wannan

Fitaccen basarake a Arewa ya magantu kan halin kunci, ya tura sako ga 'yan kasuwa kan tsadar kaya

Sun bukaci gwamnan ya tabbatar an bi tsarin da ya dace domin gabatar da limamin wanda ke da matukar tasiri, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Juma’a 1 ga watan Disamba aka bude masallacin da sallar Juma’a bayan shafe kusan shekaru biyar a kulle.

Babban dalilin kulle masallacin shi ne matsalar da aka samu da rarrabuwar kai yayin zaben limamin da zai maye gurbi a masallacin.

Lamarin ya jawo rarrabuwar kawunan wanda ke yin salla har kashe biyu a masallacin inda kowa ke bin wanda ya ke goyon baya.

Shawarar da suka bai wa Gwamna Adeleke

Shugaban limaman, Abdulrazaq Amad shi ya bayyana haka a jiya Alhamis 29 ga watan Faburairu a jihar, cewar Daily Trust.

Amad ya shawarci Gwamna Adeleke ya tabbatar an bi tsari da ka’ida na addinin Musulunci domin tabbatar da zakulo wanda ya dace da mukamin.

Kara karanta wannan

Kano: An bai wa Abba shawarar yadda zai inganta jihar kamar Sanata Kwankwaso, ya yi godiya

Ya kuma ce ya kamata gwamna ya cire hannunsa kan zaben inda ya ce akwai masu ilimi a Inisa wadanda suka san yadda ake zaban limami.

Har ila yau, Amad ya bukaci Oba na Inisa, Joseph Oyedele shima ya cire hannunsa kan lamarin domin yin abun da ya dace.

Adeleke ya nada sarki

A baya, kun ji cewa Gwamna Ademola Adeleke ya nada sabon Sarkin Iree, Yarima Ibrahim Oyelakin a jihar Osun.

Hakan ya biyo bayan tsige manyan sarakuna guda uku daga mukaminsu da gwamnan ya yi kimanin wata daya da ya wuce.

Asali: Legit.ng

Online view pixel