Fitaccen Jarumin Fina-Finai a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya da Shekaru 62

Fitaccen Jarumin Fina-Finai a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya da Shekaru 62

  • An shiga wani irin yanayi bayan sanar da rasuwar fitaccen jarumin fina-finan Nollywood a Najeriya
  • Marigayin, John Okafor ya rasu ne a yau Asabar 2 ga watan Maris a wani asibiti da ake kira Evercare
  • Marigayin wanda kafin rasuwarsa ya yi shura a masana'antar Nollywood ya rasu ya na da shekaru 62 a duniya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Shahararren jarumin fina-finan Nollywood, John Okafor ya riga mu gidan gaskiya bayan ya sha fama da jinya.

Marigayin wanda aka fi sani da Mista Ibu ya rasu ne a yau Asabar 2 ga watan Maris ya na da shekaru 62.

An babban rashi yayain da fitaccen jarumin fina-finai ya rasu a yau
Mista Ibu ya rasu ne a yau Asabar a asibitin Evercare. Hoto: John Okafor.
Asali: UGC

Yaushe aka sanar da mutuwar Mista Ibu?

BusinessDay ta tattaro cewa marigayin wanda kuma dan wasan barkwanci ne ya rasu ne a asibitin Evercare.

Kara karanta wannan

Inna lillahi wa inna illaihi raji'un, fitaccen jarumin fim ya mutu a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masoyan marigayin da dama sun tura sakwannin jaje a kafafen sadarwa musamman X bayan rasuwar jarumin.

Duk da ba a samu karin bayani kan silar mutuwar jarumin ba, amma ya sha fama da jinya wanda har ya yi sanadin yanke kafarsa.

Har zuwa lokacin tattara wannan rahoton, iyalansa da kuma wakilansa ba su yi martani kan rasuwar marigayin ba, cewar Channels TV.

Wasu daga cikin fitattun jaruman Nollywood sun jajantawa iyalan marigayin kan rasuwar jarumin.

Jarumi Sisi Quadri ya riga mu gidan gaskiya

Wannan babban rashi da aka yi a masana'antar Nollywood na zuwa ne awanni 24 bayan mutuwar jarumi Quadri Oyebamiji.

Marigayin wanda aka fi sani da Sisi Quadri ya rasu ne a jiya Juma'a 1 ga watan Maris ya na da shekaru 44 a duniya.

Abokin aikin marigayin, Tunde Olayusuf shi ya tabbatar da mutuwar marigayin a shafinsa na soshiyal midiya.

Kara karanta wannan

Dangi sun shiga makoki yayin da tuwo ya kashe mutum, aka kwantar da 4 a asibiti

An yanke wa Mista Ibu kafa

Kun ji cewa masu kula da lafiyar jarumin fina-finan Nollywood, John Okafor sun yanke kafar shahararren jarumin don ceto rayuwarsa.

Mista Ibu da iyalansa sun bukaci taimakon al'umma kan halin rashin lafiya da ya ke ciki wanda ya yi sanadiyar rasa kafarsa.

Wannan na zuwa ne bayan shafe lokaci mai tsawo ya na jinya a asibiti wanda 'yan siyasa da jarumai suka taimaka masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel