Duk da Halin Kunci da Tsadar Siminti, Kamfanin Dangote Ya Fadi Kazamar Ribar da Ya Samu

Duk da Halin Kunci da Tsadar Siminti, Kamfanin Dangote Ya Fadi Kazamar Ribar da Ya Samu

  • Yayin da ‘yan Najeriya ke kukan farashin siminti a Najeriya, kamfanin Dangote ya sanar da kazamar riba da ya samu a bangaren
  • Kamfanin ya samu ribar fiye da naira biliyan 455 wanda ya tabbatar da karin kaso 19 idan aka kwatanta da shekarar bara
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake kukan tsadar siminti a Najeriya wanda ya fara kawo cikas ga harkokin gine-gine a kasar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, AbujaKamfanin simintin Dangote ya samu ribar biliyoyin kudade a karshen shekarar 2023 da ta wuce.

Kamfanin ya sanar da samun riba har naira biliyan 455.58 wanda hakan ke nufin karin kaso 19 idan aka kwatanta da bara.

Kara karanta wannan

Jerin 'yan wasan Najeriya 15 da suka fi kwasar makudan kudi a kungiyoyinsu

Duk da kuka da tsadar siminti da ake yi, Dangote ya samu kazamar riba
Dangote ya sanar da samun ribar biliyan fiye da 400. Hoto: Dangote Group.
Asali: UGC

Ribar nawa Dangote ya samu?

Kamfanin ya bayyana haka ne a cikin wani rahoton karshen shekara da jadawalin kudade da ya fitar a karshen watan Disambar 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya tabbatar da samun karin biliyan 2.208 idan aka kwatanta da 2022 wanda ya karu da kaso 36, cewar Daily Trust.

Ribar kamfanin bayan biyan haraji ya karu da naira biliyan 553 a shekarar 2023 daga biliyan 524 a 2022.

Har ila yau, kamfanin ya sanar da naira 30 ga ko wane hannun jari idan aka kwatanta da naira 20 a shekarar da ta gabata, Nairametrics ta tattaro.

Wannan na zuwa ne yayin da ake kukan tsadar siminti a Najeriya wanda ya fara kawo cikas ga harkokin gine-gine a kasar.

Ganawar Gwamnati da Dangote, BUA

An ruwaito a kwanakin baya cewa ana siyar da simintin har fiye da N10, 000 a wasu wurare wanda ya ja hankalin mutane a kasar.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Gwamnatin Zulum ta yi wa ma'aikata sha tara na arziki, an samu ƙarin bayani

Daga bisani, Ministan Ayyuka ya yi zama da kamfanonin simintin da suka hada da Dangote da BUA da kuma Lafarge kan tsadar simintin.

Bayan ganawar Ministan da kamfanonin sun fitar da matsaya cewa za su iya rage farashin simintin zuwa N7, 000 kacal.

Tinubu ya bukaci karya farashin siminti

Kun ji cewa Shugaba Tinubu ya bukaci kamfanonin siminti da su rage farashin simintin ya koma kamar yadda ake siyarwa a baya.

Ministan Ayyuka, Dave Umahi shi ya bayyana haka inda ya ce Tinubu ya kadu da tashin farashin simintin a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel