Yayin Da ’Yan Najeriya Ke Fama da Mahara, Harbe-Harben Sojoji Ya Hallaka Mutum 2 Kan Wani Dalili

Yayin Da ’Yan Najeriya Ke Fama da Mahara, Harbe-Harben Sojoji Ya Hallaka Mutum 2 Kan Wani Dalili

  • Yayin da ‘yan Najeriya ke fama da hare-haren ‘yan bindiga da masu garkuwa, ana zargin sojoji sun yi ajalin wasu mutane babu dalili
  • Akalla mutane biyu ne suka rasu bayan harbe-harbe da sojojin suka yi a kauyen Okere da ke karamar hukumar Warri ta kudu a jihar Delta
  • Sai dai Kwamandan Bataliyar, Manjo A. Ohegbe ya fada wa ‘yan jaridu cewa bai san da maganar harbe-harben ba har zuwa wannan lokaci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Delta – Akalla mutane biyu ne aka tabbatar sun mutu yayin da sojoji suka yi harbe-harbe a jihar Delta.

Lamarin ya faru ne a kauyen Okere da ke karamar hukumar Warri ta Kudu da ke jihar Delta a jiya Asabar 2 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Yanzu Nan: Mutane sun fasa dakin ajiya, an sace buhunan abincin gwamnati a Abuja

Harin soji ya hallaka wasu mutane biyu da jikkata wasu a Najeriya
Rundunar ta musanta hallaka mutanen a jihar Delta. Hoto: Nigerian Army.
Asali: Twitter

Menene martanin rundunar kan harin?

Kwamandan Bataliyar, Manjo A. Ohegbe ya fada wa ‘yan jaridu cewa bai san da maganar harbe-harben ba, kamar yadda Abatimedia ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai Ohegbe ya ce akwai jami’an tsaro sosai yayin zayarar Olu na Warri zuwa yankin a ranar Asabar 2 ga watan Maris.

Ya ce yawan jami’an tsaron ya faru ne bayan wasu a yankin sun ki amincewa da ziyarar Olun na Warri zuwa kauyen, cewar The Discoverer Nigeria.

Su waye ake zargin sun rasa ransu?

Ana zargin wadanda ba su son ziyarar su na da alaka da Cif Ayiri Emami wanda aka tube a matsayin Ologbotsere na Warri.

Tribune ta tattaro cewa bayan kisan Macaulay Uku da Daniel Grey, mutane da dama sun samu munanan raunuka.

Wadanda suka rasa ran nasu da kuma wadanda suka samu raunuka an tabbatar da cewa su na goyon bayan Cif Emami ne.

Kara karanta wannan

Fitaccen basarake a Arewa ya magantu kan halin kunci, ya tura sako ga 'yan kasuwa kan tsadar kaya

Adeleke ya nada sabon Sarki

Kun ji cewa wata daya bayan tube wasu manyan Sarakuna uku a jihar Osun, Gwamna Ademola Adeleke ya nada sabon Sarki.

Wannan na zuwa ne yayin da gwamnan ya tube sarakunan guda uku wadanda suke da matukar girma da daraja a jihar.

Gwamnan ya nada Yarima Ibraheem Oyelakin a matsayin sabon zababben Sarkin a masarautar Iree da ke jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel