Za a Dauke Wasu Na'urori Daga Kwalejin Zaria Zuwa Legas? Gaskiya Ta Fito Bayan Zargin Dattawan Arewa

Za a Dauke Wasu Na'urori Daga Kwalejin Zaria Zuwa Legas? Gaskiya Ta Fito Bayan Zargin Dattawan Arewa

  • Kungiyar Dattawan Arewa ta zargi Gwamnatin Tarayya da shirin dauke wasu na'urori daga Kwalejin Zaria zuwa Legas
  • Kungiyar ta ce ma'aikatar jiragen sama ta na shirin dauke su ne daga Kwalejin Fasaha ta jiragen sama da ke jihar Kaduna
  • Sai dai Ministan harkokin jiragen sama, Festus Keyamo ya ƙaryata hakan inda ya ce babu kamshin gaskiya a cikinta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta karyata jita-jitar cewa za ta dauke wsasu manyan na'urori a Kwalejin Fasaha ta jiragen sama da ke Zaria zuwa jihar Legas.

Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo shi ya fayyace haka a cikin wata sanarwa a shafin Twitter a yau Litinin 4 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Bayan Dangote, jama'a sun tare motar BUA, an wawushe kayan abinci ana tsakiyar yunwa

An zargi Gwamnatin Tarayya da kokarin dauke wasu na'urori daga Arewa zuwa Legas
Gwamnatinsa Tarayya ta karyata jita-jitar dauke na'urori daga Zaria zuwa Legas. Bola Tinubu, Northern Elders Forum.
Asali: Facebook

Wane martani Gwamnatin Tarayya ta yi?

Keyamo ya ƙaryata cewa gwamnatin na shirin dauke manyan na'urorin kashe gobara daga Kwalejin zuwa jihar Legas, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tunde Moshood, hadimin Ministan a bangaren yada labarai shi ya bayyana haka inda ya ce wannan labarin kanzon kurege ne.

"Mun samu wani faifan bidiyo da ke yawo inda wani dan Majalisa ke magana kan shirin ma'aikatar na dauke na'urar daga Zaria zuwa Legas.
"Wannan labari babu kamshin gaskiyas a cikinsa kuma shiri ne kawai na masu neman ta da zaune tsaye domin cika burinsu.
"Muna bukatar al'umma da su yi fatali da wannan labari da ake yaɗawa wanda babu komai a cikinsa sai karairayi da siyasa."

- Tunde Moshood

Wannan na zuwa bayan Dattawan Arewa sun zargi shirin na dauke na'urar don kai ta jihar Legas kamar yadda aka yi a wasu ma'aikatu, cewar Ripples.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Tinubu ya tsaida ranar fara rabon abinci tan dubu 42 da jihar da za a fara

Kakakin kungiyar, Abdul-azeez Sulaiman shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa inda ya ce hakan babban ci baya ne ga Kwalejin.

Kungiyar ta ce dauke wannan na'urorin daga Kwalejin NCAT zai jawo cikas babba ga makarantar da ma hukumar jiragen saman baki daya.

Abba zai mika dajin Falgore ga Tinubu

Kun ji cewa Gwamna Abba Kabir ya amince zai mika dajin Falgore ga Gwamnatin Tarayya domin samun kulawa.

Wannan na zuwa ne bayan wata kungiya ta bukaci gwamnatin jihar ta sadaukar da dajin zuwa ga Gwamnatin Tarayya kan wasu dalilai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel