Bayan Dangote, Jama'a Sun Tare Motar BUA, an Wawushe Kayan Abinci Ana Tsakiyar Yunwa

Bayan Dangote, Jama'a Sun Tare Motar BUA, an Wawushe Kayan Abinci Ana Tsakiyar Yunwa

  • Kamfanin BUA ya tafka asara yayin da jama'a suka tare motarsa a Zariya suka wawushe gaba daya katan-katan na taliyar da ta dauko
  • Wani ganau ya shaida cewa direban motar ya tsaya a kauyen Dogarawa da nufin ya yi Sallah, inda mutanen suka sace kayan kafin ya idar
  • Rahotanni sun bayyana cewa jami'an ƴan sanda da aka tura wurin da abin ya faru, sun cafke mutum biyar da ake zargin sun saci kayan

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Zariya, jihar Kaduna - Wasu gungun jama'a sun kai hari kan wata motar BUA dauke da katan-katan na taliya a yankin Dogarawa ta hanyar Zariya zuwa Kano.

Kara karanta wannan

Dangi sun shiga makoki yayin da tuwo ya kashe mutum, aka kwantar da 4 a asibiti

Dogarawa wani gari ne da ke wajen Zariya a kan babbar hanyar zuwa Kano, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Yunwa ta sa jama'a sun wawushe katan-katan na taliyar BUA a Zariya.
Yunwa ta sa jama'a sun wawushe katan-katan na taliyar BUA a Zariya. Hoto: CVM/NAN
Asali: UGC

Yan daba sun tare tirelolin abinci a Suleja

Wannan dai yana zuwa ne mako guda bayan da wasu ‘yan daba suka tare tireloli da ke makare da kayan abinci a yankin Suleja da ke jihar Neja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Channels TV ta ruwaito cewa sun sace buhunan shinkafa da sauran kayan abinci a wani yanayi na halin kunci da ake ciki a kasar.

Tirelolin dai an ce sun nufi Abuja ne daga Kaduna, inda ‘yan barandan suka tare hanya tare da yin kone a kan titin.

Yadda jama'a suka yi wa tirelar BUA fashi

Wata majiya ta bayyana cewa al’amarin na ranar Juma’a ya faru ne da misalin karfe 3:15 na rana bayan direban motar ya ajiye ta a gefen titi domin yin sallah.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya za ta fara biyan matasa marasa aikin yi alawus, bayanai sun fito

Majiyar ta kara da cewa:

"Ko katan daya na taliyar jama'a ba su bari ba, duk sun yi awon gaba da su."

Legit ta nemi jin ta bakin rundunar 'yan sanda

An tattaro cewa, rundunar ‘yan sandan da aka tura wurin da lamarin ya faru, ta cafke mutane biyar da ake zargi.

Legit Hausa ta nemi jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sanda na jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige don jin ta bakin sa akan lamarin.

Sai dai duk wani yunkuri na magana da Jalige ya ci tura yayin da bai daga wayarsa ba kuma bai mayar da amsar sakon kar ta kwana da aka aika masa ba.

Mutane sun tare motar Dangote, sun sace kayan abinci

A wani labarin makamancin wannan, Legit Hausa ta ruwaito yadda mutane suka tare tirelar Dangote dauke da kayan abinci suka dasa wawaso.

Lamarin wanda ya faru a jihar Katsina, an ruwaito cewa motar na kan hanyar kai kayan abincin Nijar lokacin da jama'a suka tare ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel